Gwamnati ta bayar da tallafin kayan abinci ga gidan marayu na Kirista da ke unguwar Tumfure a Jihar Gombe.
Wannan dai na zuwa ne bayan wani rahoto da Aminiya ta wallafa kan cewa gwamnatin jihar ba ta waiwayar gidan marayun.
Ana iya tuna cewa, shugaban gidan marayun, El-Polycarp Yusuf Degree ne ya soma korafi kan yadda gwamnati ta manta da su a yayin da wasu matan ’yan sanda da ke shalkwatar ’yan sandan Gombe suka kai wa gidan marayun tallafin kudi da abinci.
Kimanin wata guda da wannan korafi, sai ga shi a karo na biyu ke nan gwamnatin tana rabon kayan tallafin a gidan marayu na Kirista da kuma gidan marayu na Al-Gidan Umma Hajara (AL-Guh).
A zantawarsa da wakilinmu, shugaban gidan marayun wanda kuma shi ne Babban Sakataren Gidajen Marayun na Kirista da ke Najeriya, El-Polycarp Yusuf Degree, ya bayyana farin ciki marar misaltuwa da samun tallafin wanda a cewarsa bai taba tsammani ba.
El-Polycarp Degree, ya ce tun da aka bude gidan Marayun ba su taba samun kowane irin tallafi ba sai ga shi da suka koka duniya ta ji, gwamnati ta tuna da su don haka ba su da abin yi face yi wa gwamnatin godiya.
Ya ce “ban san yadda aka yi sunanmu ya shiga jerin kungiyoyin da za a rabawa kayan abincin ba, domin ba mu san ta inda za mu mika kokenmu ba amma da ’yan jarida suka dauki labarin sai ga shi gwamnati ta ji kukansu.”
Kazalika, ya yi kira ga masu hannu da shuni da su rika bibiyar gidajen marayu domin sanin halin da suke ciki su taimaka musu.
“Barin yara da yunwa musamman marayu jefa masu arziki cikin rashin kwanciyar hankaki, saboda haka marayu na bukatar kulawar al’umma.”
Ya ce yana fatan irin wannan tallafi na gwamnati ya dore wanda za su rika samu a duk lokacin da za a taimaka wa kungiyoyi su ma ya zama suna ciki.
Aminiya ta ruwaito cewa, kungiyoyi 130 ne suka samu tallafin cikinsu har da gidan marayun Kiristan da ya samu tallafin buhunan shinkafa mai nauyin kilo 10 guda 100.