✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bayan nasarar Tinubu, Atiku ya shiga tattaunawa da Gwamnonin PDP

Taron na zuwa ne bayan Tinubu ya zama dan takarar APC

Yanzu haka dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yana can yana tattaunawa da Gwamnonin jam’iyyar a Abuja.

Taron dai na zuwa ne bayan tsohon Gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben fitar da gwanin jam’iyyar a zaben 2023.

Aminiya ta gano cewa babban makasudin taron shi ne yadda za a zabi wanda zai zama dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na jam’iyyar.

Sauran batutuwan sun hada da kafa Kwamitin Yakin Neman Zaben dan takarar, batun zaman Tinubu dan takarar APC da kuma hanyoyin da za a bi wajen kwace mulki daga APC.

Daga cikin Gwamnonin da ke halartar taron akwai na Bayelsa, Douyi Diri da na Bauchi, Bala Muhammed da na Ribas Nyesom Wike, da kuma na Binuwai Samuel Ortom.

Sauran sun hada da na Sakkwato Aminu Tambuwal da takwaransa na Oyo, Seyi Makinde.