Majalisar Shura ta kungiyar ISWAP, ta nada Sani Shuwaram, mai kimanin shekara 45 a matsayin sabon shugabanta na yankin Tafkin Chadi, wato Wali.
Nadin nasa na zuwa ne ’yan watanni bayan mutuwar tsohon shugabanta, Abu-Mos’ab Al-Barnawi.
Kafar yada labarai ta PRNigeria ta rawaito cewa nadin nasa ya biyo bayan amincewa daga hedkwatar kungiyar ISIS da ke kasar Iraki a watan Augusta.
A na dai ganin Shuwaram a matsayin wanda sunansa bai shahara ba sosai a kungiyar.
Alkalin kungiyar, Bukar Arge ne ya rantsar da Shuwaram a wani kwarya-kwaryar biki da aka yi a wani sansanin kungiyar da ke Kurnawa, wanda ake gani a matsayin karamin sansaninta da ke kusa da tafkin Chadi, ban da wanda ke Karamar Hukumar Abadam ta Jihar Borno.
Shuwaram dai shi ne zai kasance Shugaban kungiyar na biyar bayan Mamman Nur da Abu-Mosab Albarnawwy da Abbah-Gana da Abu-Dawud, wanda aka fi sani da Abu Hafsat Al-Ansari da kuma Aba-Ibrahim.
Nadin nasa dai na nufin shi ne zai ci gaba da jagorantar ayyukan ta’addancinta a Sambisa da Timbuktu da Tumbumma da ma wasu wuraren, karkashin kulawar Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurashi, babban Shugaban ISWAP a Iraki.