✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan karbar kudin fansa, ’yan bindiga sun ki sako Daliban Tegina

Kwana biyu bayan karbar kudaden da aka yi karo-karo, masu garkuwa sun ki sakin yaran.

’Yan bindigar da suka sace dalibai kimanin 150 da makarantar Islamiyya a Tegina, Jihar Neja sun karbi kundin fansa daga iyayen yaran amma sun ki sako musu ’ya’yan nasu.

Binciken wakilinmu ya gano cewa rashin sako yaran, kwana biyu bayan iyayensu sun biya masu garkuwar Naira miliyan 20, ya kara jefa iyayen cikin tashin hankali.

Majiyoyinmu a Masarautar Kagara da kuma garin Tegina sun tabbatar mana cewa an ba wa ’yan bindiga kudin, a yayin da wa’adin da suka bayar na makon jiya ya kare.

“Ina tabbatar muku yau kwana biyu ke nan da aka ba su Naira miliyan 20 a gida biyu —Naira miliyan 10 sau biyu — amma har yanzu ba su sako yaran ba. Mun kara shiga damuwa, ”inji wata majiya a Majalisar Masarautar Kagara.

Daya daga cikin iyayen daliban da aka sace a Tegina ya tabbatar wa wakilin namu cewa da kyar iyayen suka iya tara N20 miliyan da aka kai wa masu garkuwar.

“Sun yi alkawarin sakin ’ya’yan namu bayan sun karbi kudaden, amma muna cikin damuwa saboda yanzu kwana biyu ke nan amma ba su yi hakan ba,” inji mahaifin wanda ya bukaci a sakaya sunansa saboda tsoro.

Da farko Naira miliyan 200 masu garkuwar suka nema, amma daga baya suka rage zuwa Naira miliyan 50, kafin daga karshe suka tsaya a kan miliyan 30.

Amma Gwamnatin Jihar Neja ta ce ba za ta biya ’yan bindiga kudin fansa ba, lamarin da ya sa iyayen daliban neman taimako a masallatai da coci-coci, tare da sayar da kadarorinsu domin hada Naira miliyan 30 din, amma abun ya gagara.

Wasu rahotannin kafafen yada labarai sun ce uku daga cikin daliban sun rasu a hannun masu garkuwar, da yawa daga cikin sauran kuma suna fama da tsananin rashin lafiya, wun kuma galabaita saboda sanyi da yunwa.

Amma majiyarmu ta ce sun dauki labarin a matsayin ji-ta-ji-ta saboda babu tabbacin hakan daga masu garkuwar.

Da aka tuntubi kakakin Gwamnan Jihar Neja, Mary Noel Berje, ta ce gwamnatin jihar ba ta san da biyan kudin fansa da iyayen suka yi ba ko kuma mutuwar uku daga cikin daliban da aka sace.

Ta sake jaddada matsayin gwamnatin jihar na kin biyan kudin fansa ga masu garkuwa.