✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan cece-kuce, Naziru Sarkin Waka ya ba ‘Tambaya’ kyautar N2m

Sarkin Waka dai na cikin wadanda suka goyi bayan Tambayan a wancan lokacin.

Bayan shafe kwanaki ana ta cece-kuce kan batun biyan hakkokin ’yan wasa a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Naziru Sarkin Waka, ya ba jaruma Ladin Cima, wacce aka fi sani da Baba Tambaya kyautar Naira miliyan biyu domin ta ja jari.

Hakan na zuwa ne bayan jarumar, yayin wata hirarta da Sashen Hausa na BBC a makon da ya gabata ta yi korafin cewa ba a taba ba ta sama da N2,000 zuwa N5,000 a matsayin kudin aiki ba, tun da take fitowa a fim.

Lamarin dai ya tayar da kura a lokacin, inda wasu masu shirya fina-finai a masana’antar suka musanta ikirarin nata.

Sarkin Waka dai na cikin wadanda suka goyi bayan Tambayan a wancan lokacin.

To sai dai a wani sabon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, Naziru ya yi alkawarin ba ta kyautar kudaden domin ta ja jari ta kuma magance wasu daga cikin matsalolinta.

Naziru dai a wancan lokacin ya yi zargin cewa akwai wadanda ma suke fitowa a fim din a kyauta, da kuma matan da ma ya yi zargin ana ‘amfani da su’ kafin su fito a fim.