✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun zaben abokan takarar Atiku da Tinubu ya tayar da kura

An samu baraka tsakanin gwanoni da shugabannin PDP, batun hada Musulmi biyu a APC ya jawo surutai.

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyar PDP, Atiku Abubakar da abokin karawarsa na Jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu suna nazarin mutumin da kowannensu zai dauka a matsayin abokin takara a zaben 2023.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Zabe Ta Kasa (INEC) ta sanar da 17 ga watan Yuni da muke ciki a matsayin ranar karshe ta mika mata sunayen ’yan takarar.

A halin da ake ciki, bangarorin manyan jam’iyyun biyu na kokarin ganin daga cikinsu ’yan takarar mataimakin shugaban kasan za su fito.

Tun bayan kammala zabukan fitar da ’yan takarar shugaban kasa na manyan jam’iyyun biyu, APC da PDP, hankula suka karkata zuwa batun zabin abokan takararsu.

Masu sharhi na ganin zabin abokan takarar manyan ’yan siyasar biyu na da matukar tasiri wajen cin zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Wani mai sharhi kuma asanin Kimiyyar Siyasa daga Jami’ar Abuja, Dokta Abubakar Umar Kari, ya ce, “Abubuwa da dama sun ta’allaka ne da zabin abokan takararsu da kuma yadda suka iya samun goyon baya da hadin kan muhimman mutane da bangarori, musamman wadanda ba su ji dadin yadda sakamakon zabukan ’yan takarar shugaban kasa suka kasance ba.” 

A halin da ake ciki, gwamnoni da shugabannin jam’iyya, wadanda su ne su ne suka fi karfin fada a ji a jam’iyyun biyu, suna fadi-tashin ganin yadda za a zabo ’yan takarar.

Majiyoyi masu tushe sun ce PDP da APC na duba yiwuwar zabo wasu gwamnoni masu ci su zama abokan takarar Atiku da Tinubu.

Baraka tsakanin gwamnoni da Uwar Jam’iyyar PDP

Aminiya ta gano wata sabuwar baraka da ta kunno kai a Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar PDP kan zabin abokin takarar Atiku.

Atiku na duba yiwuwar daukar Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin mataimaki.

Amma Gwamnan Jihar Ribas Nysom Wike, wanda shi ne ya zo na biyu a zaben fitar da dan takarar shugbaban kasa na PDP, yana kwadayin zama abokin takarar Atiku.

A gefe guda kuma akwai bangaren jam’iyyar da ke son ganin an dauki Gwamna Udon Emmanuel na Jihar Akwa Ibom.

Wani dan jam’iyyar ya ce shigar Wike cikin masu son zama mataimakin shugaban kasa ya kawo rabuwar kai a tsakanin gwamnoni da hedikwatar jam’iyyar.

“In banda Shugaban Jam’iyya na Kasa, kusan duk mambobin Kwamitin Gudanarwa na jam’iyyar suna goyon bayan Wike ya zama abokin takarar Atiku, saboda irin gudunmmawar da ya bayar wajen dorewar jam’iyyar.

“Haka aka samu irin wannan rabuwar kai a tsakanin gwamnonin jam’iyyarmu su 13; mutum shida zuwa bakwai daga cikinsu suna goyon bayan Wike,” inji shi.

Wata majiya daga PDP ta ce jam’iyyar ta kafa wani kwamitin dattawa da zai taimaka wajen zabo dan takarar mataimakin shugaban kasa.

“Daga cikin mambobin kwamitin akwai tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Janar Aliyu Gusau; Su ne za su zabo mutumin da zai yi tasiri a zabe wanda kuma kowa zai yi na’am da shi,” inji majiyar.

Wani mamban Kwamitin Amintattun PDP ya tabbatar wa wakilinmu da cewa an kafa kwamintin dattawan, wanda ya ce yana tuntubar bangarorin jam’iyyar domin tabbatar da an zabo mutumin da kowa zai yi na’am da shi.

“Ba zan yaudare ku ba, ana ci gaba da tuntuba, amma ba a kammala ba, kuma ana tafiya ne tare da kowane bangare,” inji shi.

Yiwuwar Tinubu ya dauki Zulum

A bangare APC kuma, majiyoyi masu kusanci da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu, sun bayyana cewa yana duba yiwuwar dauko Musulmi a mastayin abokin takararsa.

Bangaren Tinubu na son a maimata abin da aka yi a zaben 1993, inda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP, Cif MKO Abiola, ya dauko Babagana Kingige, Musulmi daga Jihar Borno a matsayin abokin takararsa.

Wani na hannun daman Tinubu ya ce ba don surutan da za a yi ba, tsohon Gwamnan Jihar Legas din ya fi son Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya zama abokin takararsa.

“Zabin da ya fi mana shi ne hada Musulmi biyu, saboda mataimakin shugaban kasa ba shi da karfi sosai kamar yadda mutane ke magana. Shi safaya ne. Abin da ya fi muhimmanci shi ne kujerar shugaban Majalisar Dattawa.

“Na biyu kuma, matar Tinubu Kirista ce kuma Fasto ce a Cocin Redeem; Sanin kowa ne cewa matar Tinubu ’yar siyasa ce kuma ’yar Majalisar Dattawa ce tun 2011. Saboda haka babu wani abin damuwa,” inji majiyar.

Shi ma wani daga bangaren Tinubu ya yi yin Muslim-Muslim a APC abu ne da babu makawa.

“Na yi imani za mu kayar da Atiku idan muka yi abin da ya dace,” inji shi.

Amma kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta gargadi jam’iyyun siyasa da cewa su guji tsayar da mutum biyu masu bin addini daya a matsayin ’yan takararsu na shugaban kasa da mataimakinsa.

Sakataren CAN na Kasa, Joseph Bade Daramola, ya ce yin hakan na iya kawo barazana ga dimokuradiyyar Najeriya mai tattare da barazana iri-iri.

Da yake taya Tinubu da Atiku murnar cin zaben ’yan takarar shugaban kasa, Joseph ya shawarci Tinubu ya zabo abokin takara Kirista daga Arewa, Atiku kuma ya zabo Musulmi daga yankin Kudu.

Abin takaici ne fifita addini a kan kwarewa —El-Rufai

Amma a nasa bangaren, Gwamna Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana takaici kan yadda ake fifita batun bambancin addini a siyasar Najeriya.

A cewar El-Rufai, abin da ya fi muhimmanci shi ne kwarewar mutum da iya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na shugaba, ba wai addininsa ba.