✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun yara miliyan 10 da ba sa zuwa makaranta

Babban Sakataren riko na Hukumar Ilimin Baidaya na kasa (UBEC), Farfesa Charles Onocha ya ce fiye da yara miliyan goma ba sa zuwa makarantar firamare…

Babban Sakataren riko na Hukumar Ilimin Baidaya na kasa (UBEC), Farfesa Charles Onocha ya ce fiye da yara miliyan goma ba sa zuwa makarantar firamare a Najeriya. Wannan matsalar kuma ta shafi dukkan jihohin kasar nan har da Abuja.
Ya ce, an yi shakulatin-bangaro da wadannan yaran, wanda kuma bai kamata a yi musu haka ba, kamata ya yi a ba su dukkan kulawar da suke bukata ciki har da ilimi, yin hakan zai sanya su amfani al’umma da kuma kasa baki daya.
Bayan Farfesa Onocha ya yi wannan batun ne, sai Shugaban Kwamitin Ilimi na Majalisar Dattawa, Sanata Uche Chukwumereji ya ce, Gwamnatin Jihar Neja ce kawai ta ba Hukumar UBEC kudin gudanarwa har zuwa shekarar 2015.
Batun rashin zuwan yara makarantun firamare abin tashin hankali ne, kuma ya kamata a shawo kansa da gaggawa. Onacha ya ce, shirin UBEC ya shafi yadda za a zamanantar da makarantun almajirai da shirin ba da ilimi kyauta ga mata da kuma shawo kan yaran da suka daina zuwa makarantun firamare a shiyyoyin Kudu maso Gabas da kuma Kudu maso Kudu.
Kodayake wata majiya ta bayyana ba a ba hukumar isasshen kudin da za ta gudanar da wadannan ayyukan ba.
A bara Hukumar UBEC ta karbi Naira biliyan 177 don ta gudanar da ayyukan da suka shafi makarantun firamare, inda kuma hukumar ta ce tuni ta  raba Naira biliyan 142.700 ga jihohi da kuma Abuja. Hakan ya nuna an bayar da kashi 80.67 na kudin.
Batun gaskiya shi ne, ya kamata a shawo kan matsalar rashin zuwan yara makaratun firamare da wadannan kudaden da aka ba jihohi da Abuja, ya kamata jihohi su mayar da hankali kan ilimin firamare domin hakan zai sanya matsalar ilimi ta ragu sosai.
kananan hukumomi wadanda suka fi kusa da talakawa sun kasa taka rawar da za ta taimaka wa ilimin makarantun firamare. Gwamnatin jihohi wadanda a halin yanzu suke rike da asusun hadin gwiwa tsakaninsu da kananan hukumomi, wadanda kuma hakkin horar da malamai, sanya idanu, samar  da kayayyakin koyarwa da kuma samar da ajujuwa suka rataya a kansu ba su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ba.
Saboda gazawar da jihohi suka yi ne ya sanya ajujuzuwa suka lalace, aka kasa gyara su, ko a gina sababbi ko kuma a zamanantar da gine-ginen makarantun firamare, hakan ne kuma ya sanya aka kasa ganin amfanin kudaden da UBEC take karba.
An sace kudaden da aka ware don ilimin firamare, inda kuma yara ke zaune a kan dandamali, wani lokaci ma a karkashin bishiyoyi kafin su dauki karatu. Bugu da kari albashin malamai ya yi kadan wanda ya sanya suke gudanar da harkokin kasuwanci don su ciyar da iyalansu da biyan kudin haya da zirga-zirga da sauransu, wanda kuma hakan ya dauke musu hankali daga koyarwa. Rashin zuwa wurin aiki da malamai suke yi ya sake mayar da hannu agogo baya, domin ko da yaran sun je makaranta ma babu malamai.
Wadansu suna ganin Hukumar UBEC wata kafa ce ta bunkasa cin hanci da rashawa. Dalilin kuwa shi ne, gwamnoni kan zabi ‘yan gaban goshinsu su nada su shugabannin hukumomin UBEC, sannan su rika ba su kudi a matsayin sakayya kan yakin da suka yi musu lokacin zabe ba tare da sun rika lura da yadda ake gudanar da makarantun firamaren ba.
A kwanakin nan an samu rahoton sakamakon jarrabawa, inda Jihar Barno da Yobe da Adamawa da Sakkwato da kuma Zamfara suke kan gaba wurin faduwar jarrabawa. Ga batun yaran da suke barin makaranta don kama kasuwanci a shiyyoyin Kudu maso Gabas da kuma Kudu maso Kudu ma abin tashin hankali ne.
Ya kamata a kirkiro dokar za a rika ladaftar da hukumomin UBEC da ba sa gudanar da ayyukansu kamar yadda suka kamata. Hakan zai sanya a rika taka tsan-tsan, zai kuma taimaka a samu sa’ida kan matsalar da ta yi cacukwi da ilimin firamare.
Miliyan goma ba kadan ba ce, hakan zai haifar da aikata miyagun laifuffuka, don haka ya zama dole a shawo kan matsalar, don hana faruwar hakan nan gaba.