✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun tsarin fanshon Akpabio

A makon jiya ne Majalisar Dokokin Jihar Akwa Ibom ta amince da dokar da ta halarta ba gwamna da iyalinsa fansho bayan ya bar mulki…

A makon jiya ne Majalisar Dokokin Jihar Akwa Ibom ta amince da dokar da ta halarta ba gwamna da iyalinsa fansho bayan ya bar mulki har zuwa karshen rayuwarsa. Kodayake ba wannan ne karo na farko ba, wadansu jihohi ma sun amince da dokar ba tsofaffin gwamnoni fansho, sai dai na Jihar Akwa Ibom din ya bambanta da na sauran jihohi. Wannan kudirin dai tuni ya zama doka, domin tuni ’yan majalisar jihar suka sanya masa hannu. Dokar ta bayyana Akpabio da iyalinsa za su rika samun makudan kudi bayan ya sauka daga mulki. Dokar dai ta amince a rika ba mataimakin gwamna da iyalinsa fansho sai dai nasu ba zai taka kara ya karya ba.
Dokar ta amince gwamnatin Jihar Akwa Ibom za ta rika ba Akpabio fanshon Naira miliyan 100 kowace shekara, za ta rika saya masa mota duk bayan shekara 4 da Naira miliyan 5 kowane wata don ya biya ma’aikatansa da jami’an tsaronsa da sauran abubuwan da suka shafi tsaronsa. Dokar ta kuma amince za a saya masa gida a Abuja da alawus din kashi 300 na albashinsa na shekara duk bayan shekara 4, gwamnatin jihar za ta rika saya masa mai, inda za ta rika ba shi kudin man daidai da kashi 300 na albashinsa.
Bai tsaya a nan ba, Akpabio zai rika karbar kashi 100 na albashinsa wajen biyan kudin wutar lantarki da ruwa da sauransu, sannan za a rika ba shi kashi 100  fanshonsa na shekara wajen nishadi. Sannan jihar za ta dauki nauyin bikin binne gawarsa da zaman makoki, wanda adadin kudin zai yi daidai da albashin gwamna mai ci na shekara 1. Baya ga haka ga sauran alawus-alawus za a rika ba shi lokaci zuwa lokaci.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Akwa Ibom Mista Sam Ikon a lokacin da yake sanya wa dokar hannu ya ce, sun amince da dokar ne kasancewar idan aka yi hakan zai taimaka gwamnoni da mataimakansu don su jajirce wajen yin ayyukan ci gaba, ba tare da tunanin yadda rayuwarsu za ta kasance bayan sun bar mulki ba.
Wani abin mamaki shi ne, don majalisar ta tabbatar da gaske take ne ma ya sa ta sanya hannu a dokar cikin kasa da awa 24 da mika mata kudirin.
Jihar Akwa Ibom tana samun Naira biliyan 15 daga Asusun Gwamnatin Tarayya kowane wata, baya ga haka ga kudin shiga da jihar take samu, idan aka yi la’akarin da kudin da jihar take samu da kuma ci gaban da jihar take samu sai a ga ba a samu ci gaban a zo a gani ba. Jama’ar jihar suna fama da talauci, babu abubuwan more rayuwa.
Yin hakan kwata-kwata bai dace da doka ba, idan za a duba dokar Hukumar Kudin Shiga da Haraji da Fansho da kuma Raba kudin shiga (RMAFC) ta bayyana za a rika ba da fansho ne ga ma’aikatan gwamnati da masu damarar da sauransu. Majalisar Dokokin ba ta kuma yi batun idan badi Akpabio ya zama sanata tun da an fara rade-raden zai nemi takara, shin za a ci gaba da biyansa fansho, a lokaci guda a rika biyansa hakkokin da zai samu a majalisar tarayya?
Idan kuwa haka ne za mu iya cewa wannan doka ce ta son kai ba tare da an yi la’akari da talaucin da jama’ar jihar suke ciki ba. Babu batun bambance batun yin aiki ko rashin aiki daga ’yan siyasa ba. Don haka ne ya kamata jihohin da suka sanya hannu a kan wannan dokar su dakatar da ita.
Ya kamata Hukumar RMAFC ta tashi tsaye don tabbatar da doka da oda kan  abin da ya shafi fansho a kasar nan. Kodayake hukumar kwadajo ta jihar Akwa Ibom ta ce za ta gudanar da zanga-zanga kan batun, inda ta ce abu ne da aka yi shi ‘ba tare da ka’ida ba kuma ya zarce tunani.’ kungiyar kwadagon ta ce idan aka hada wannan kudin da za a biya Akpabio ya isa a biya tsofaffin malam makaratar firamare da tsofaffin ma’aikatan gwamnatin kananan hukumomin jihar fansho da garatutinsu. A watan Yuni, shekarar 2012 Gwamnatin Jihar Akwa Ibom  ta saya wa Akpabio jirgin sama a kan Dala miliyan 45 don amfanin kashin kansa. Abin tambaya a nan shi ne, wa zai mallaki jirgin bayan ya sauka daga mulkin jihar?
Mun tabbata a yanzu ba Akpabio ba ne kawai yake da burin samar da irin wannan dokar a jihohinsu, idan kuwa hake ne ana gab da fada wa cikin wani mummunan hali a kasar nan. Don haka ya kamata a samar da dokar da za ta hana gwamnoni yin dokar da za ta amfane su kawai, ba wai talakawa ba.
A tabbata an yi kundin tsarin mulkin da zai hana ’yan siyasa yin abubuwa na kashin kansu da son kai da kuma yin abubuwan da za su wuce kima.