Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewar ya yanke jiki ya faɗi har aka kai shi asibiti a ƙasar waje.
Ya ce wannan ƙarya ce da maƙiyansa na siyasa suka ƙirƙira don kawar da hankalin mutane.
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta
- Fitaccen malami Dokta Idris Dutsen Tanshi ya rasu
Wike, ya yi wannan bayani ne a Abuja a ranar Alhamis yayin da ya kai ziyara wajen wani aiki da ake shirin ƙaddamarwa a watan gobe domin bikin cikar Shugaba Bola Tinubu shekara biyu a mulki.
A wata sanarwa da daraktan yaɗa labaransa, Anthony Ogunleye, ya fitar, Wike ya ce waɗanda ke yaɗa wannan labari suna ƙoƙarin juyar da hankalin jama’a daga batun da tsohon shugaban ma’aikatan Jihar Ribas ya fallasa na yunƙurin saka bam a majalisar dokokin jihar da kuma hari kan kadarorin gwamnati.
“Babu inda na yanke jiki na faɗi, balle har a fitar da ni zuwa ƙasar waje.
“Ko a ranar da Shugaba Tinubu ya yi buɗa-baki kan zagayowar ranar haihuwarsa na halarta.
“Haka kuma, a ranar Sallah na jagoranci mazauna Abuja zuwa taya shi barkar da sallah. Ba zan damu da irin waɗannan jita-jitar siyasa ba, kuma ba za su hana ni aiki ba,” in ji Wike.