✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun magance matsalar mahalli a Najeriya

Kwamitin da Gwamnatin Tarayya ta kafa kuma ta ba shi aikin tantancewa da mayar da Gidajen Gwamnatin Tarayya na kasuwanci, ya bayyana cewa Hukumar Kula…

Kwamitin da Gwamnatin Tarayya ta kafa kuma ta ba shi aikin tantancewa da mayar da Gidajen Gwamnatin Tarayya na kasuwanci, ya bayyana cewa Hukumar Kula Da Gidajen Gwamnatin Tarayya ta iya gina gidaje dubu 37 ne kacal a fadin kasar nan, a cikin shekaru 40. Wannan ya nuna cewa ana gina gidaje 1000 ne kadai a duk shekara ga ’yan Najeriya. Haka ke nuna dalilin da ya sanya ake fuskantar karancin mahalli a kasar nan, musamman ma an kiyasta cewa akwai karancin gidaje miliyan 17 a Najeriya. Kodayake ma a kasar kamar Najeriya, inda ake gudanar da al’amura ba tare da kididdiga ta ainahi ba, yana da wuya ma a iya gano hakikanin yawan gidajen da al’umma ke bukata, balle ma a iya gano matsalar ta sosai dangane da haka.
Abin da ke kashin gaskiya dangane da muhalli shi ne, tabbas akwai matsalar karancin muhalli a sassa daban-daban na kasar nan. Mutane na tsananin bukatar muhallai nakwarai, inda za su adana hakarkarinsu. A ta dalilin kamfar gidaje, mutane sun bige da zama a wulakantattun muhallai, wasu kuma suna zama a hanyoyin ruwa da sauransu, wanda haka babban hadari ne ga rayuwar al’umma.
Ganin yadda al’amarin muhalli ya tabarbare a kasar nan, labarin da aka samu a yanzu yana faranta rai, inda aka samu bayanin cewa Gwamnatin Tarayya ta samo lamunin Dala miliyan 300 daga kungiyar Bunkasa Muhalli Ta Duniya, inda za a yi amfani da su wajen bayar da bashin gina gidaje ga ’yan kasa. Da wannan kudin ne ake son rarraba wa ’yan kasa bashin gina gidaje ta hannun bankuna. Duk da cewa wannan yunkuri ya dace, amma ya dace gwamnati ta kara wani yunkurin, domin kuwa girman matsalar karancin muhalli ta ta’azzara, don haka ana bukatar babban yunkuri. Bisa ga haka, kamata ya yi a hada wannan yunkuri na bashi tare da gina wasu gidajen sosai, ta yadda za a jefi tsuntsaye biyu da dutse daya. Akwai bukatar lallai a tallafa wa al’umma su samu ingantattun muhalli, su huta da zama cikin wulakantattun gidaje. Inganta muhallin al’umma zai rage kazanta da kazantattun muhallin da ’yan kasa ke rayuwa a cikinsu.
Ba Gwamnatin Tarayya kadai ba, ya dace sauran gwamnatoci, musamman na jihohi da na kananan hukumomi su mike tsaye, su ma su sanya hannu wajen fito da tsare-tsare masu inganci, wajen samarwa da inganta muhallai ga ’yan kasa, domin kuwa kisan baki sai gayya.
Ya dace a maida hankali wajen inganta da tsara muhallin al’umma, a gyara hanyoyi da magudanan ruwa, sannan a samar da ingantattaun gidajen da suka dace da zaman al’umma, a kayatar da su da shuke-shuken itatuwa da fulawoyi. Idan an duba yadda kauyuka da karkara ke tasowa, ya dace a tsaya kai da fata wajen tsara muhallansu, ta yadda za su dace da tsarin da ake samu a birane. Wannan ne zai sanya idan har sun tumbatsa, ba za a samu cinkoso da kazanta ba, kamar yadda ake samu a yanzu.
Idan aka yi la’akari da matsalar mulalli a kasar nan, lokaci ya yi da ya kamata gaba daya a hada hannu, a sa himma, a magance matsalar muhalli. daya daga cikin ma’aunan da ake dubawa a ce kasa ta ci gaba, shi ne a ce al’ummarta tana da ingantattun muhalli, muhallin da ya dace a kira shi muhallin dan Adam. Babu yadda za a yi a ce wai kasa tana ci gaba, har ma tana tokabo da cewa tattalin arzikinta yana bunkasa, amma a daya hannu kuma al’ummarta na zaune cikin datti da kazanta, cikin wulakantattun gidaje marasa inganci. Wannan ba ci gaba ba ne, ci baya ne kuma babbar matsala ce. Saboda haka, ya dace dai a mayar da hankali wajen samarwa da inganta muhalli ga al’ummar kasar nan.