✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun hana gina masallaci a jami’ar Jihar Ribas

A kwanakin baya ne jaridu suka rawaito labarin Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ribas ta hana gina masallaci a jami’ar.A rahoton, an bayyana jami’ar…

A kwanakin baya ne jaridu suka rawaito labarin Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ribas ta hana gina masallaci a jami’ar.
A rahoton, an bayyana jami’ar ta bayar da kudi don gina coci-coci na mabiya darikun Kirista, a lokaci guda kuma ta rushe masallaci da kuma duk wani wuri da dalibai Musulmi suka gina da kudinsu a jami’ar.
dalibai Musulmin sun ce ba sau daya ba suka tura korafinsu ga hukumar jami’ar, bugu da kari sun tura korafinsu ga Gwamnan Jihar Ribas, Mista Rotimi Ameachi a shekarar 2008, amma har yanzu ba a share musu hawayensu ba.
Idan ba za a manta ba a watan Janairun bara ne dalibai da malaman addini suka yi zanga-zanga sakamakon rushe masallaci da hukumar jami’ar ta yi. Al’amarin da jami’ar ta sake yin kunne kashi da shi.
A wasikar da daliban suka tura wa gwaman, sun nemi ya kawo karshen al’amari, ya kuma tsawata a daina dakile wa Musulmi hakkinsu na ci gaba da yin addininsu ba tare da tsangwama ba.
“Muna gudanar da ibadunmu a cikin wani tanti ne, wanda a kullum ke fuskantar barazana daga hukumar makaranta, inda a ranar 15 ga watan Mayu 2005 suka rushe mana tantin da hade da yin awun gaba da kayayyakinmu.” Inji wasikar daliban.
Ko a yanzu da Aminiya take wannan rubutun har yanzu gwamnan bai yi wani yunkuri don a gina wa Musulmin jami’ar masallaci, ko a ba su kulawa kamar yadda aka yi wa takwarorinsu Kirista ba.
Shekara sha daya ke nan dalibai Musulmin suke fafutikar gwamnati ko hukumar makaranta su gina musu masallaci, amma hakarsu ba ta cim ma ruwa ba, hakan ne ya sanya suka tashi tsaye suka kulla taro da sisi har suka fara gina masallaci, sai dai kwana daya bayan sun fara ginin sai hukumar ta rushe shi hade da kwace musu sauran kayayyakinsu.
Abin takaicin shi ne, yadda hukumar jami’ar ta yi mirsisi wurin yin biyayya ga hukuncin da wata kotu ta yanke.
dalibai Musulmin jami’ar 98 sun shigar da kara gaban Babbar Kotu da ke garin Fatakwal, inda suka nemi kotu ta tirsasa wa hukumar jami’ar ta ba su ‘yancin gina masallaci. A karar mai lamba FHC/PHC/CS150/2012, daliban sun ce hukumar jami’ar ta hana su filin da za su gina masallaci, wanda hakan ya saba wa kundin tsarin mulki da ya ba ‘yan kasa damar yin addininsu a ko’ina suke a Najeriya.
A ranar 19 ga watan Fabrairu, 2013 Mai shari’a, Lamba Akanbe ya yanke hukunci a ba dalibai Musulmin damar gina masallaci, sannan ya umarci hukumar makaranta ta ba su filin da za su gina masallacin, amma har zuwa yanzu hukumar makaranta ba ta aikata hakan ba. A takaice dai har yanzu hukumar jami’ar tana jan kafa hade da kange duk wata hanya da dalibai Musulmin za su kai ga mallakar filin da za su gina masallaci.
Abin mamakin ma shi ne, a ce kamar jami’a da ake ganin duk wanda yake cikinta ya fahimci yaya rayuwar duniya take, amma a ce kuma a nan ake samun irin wadannan matsaloli da suka hada da nuna bambancin addini. Lallai hakan abin takaici ne.
Rashin daukar kwakkwaran mataki da gwamnatin Jihar Ribas ta yi duk da cewa an rubuta mata wasika abin takaici da daure kai ne. Bai kamata gwamnatin al’umma ta yi haka ba, kowa nata ne.
Bai kamata hukumar jami’ar ta dauki matakin hana gina masallaci ba. Kada a manta akwai majami’u shida a cikin jami’ar, wanda kuma dukkansu hukumar jami’ar ce ta yi uwa da kaka wurin gina su. Amma sai hukumar jami’ar ta hana filin da dalibai Musulmin suka ce da kudinsu za su gina, amma hakan ya gagara. Da haka ne ake tsammanin za a samu fahimtar juna idan mabiya addini kaza ba su da rinjaye to ba za su samu ‘yancin gina wurin ibadunsu ba?
Lokaci ya yi da ya kamata  a fahimci ci gaba da nuna bambancin addini ba zai kai haifar mana da da mai ido ba.