✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun faduwar farashin albarkatun man fetur

Farashin albarkatun man fetur ya fadi a duniya da kashi 18 cikin dari a kwanakin baya. Farashin ya sauka zuwa dala 95 ga kowace gangar…

Farashin albarkatun man fetur ya fadi a duniya da kashi 18 cikin dari a kwanakin baya. Farashin ya sauka zuwa dala 95 ga kowace gangar danyen mai. Abubuwa da dama ne suka haddasa faduwar farashin, wadanda suka hada da rage sayen man da Nahiyar Turai ta yi, a sakamakon karayar tattalin arziki da ta fada mata a shekarun baya. Akwai kuma batun tattalin arzikin kasar China da ya dan fadi, sannan kuma ga shi Amurka ta rage sayen danyen mai, a dalilin karuwar hako man da kamfanin Shale ya yi. Wadannan abubuwa da suke faruwa kuma ba za su rasa nasaba da matakan da Saudi Arebiya ke dauka ba, na ganin ta tsare kambinta na kasar da ta fi kowacce fitar da danyen mai a duniya.

Ga kasashen da suka dogara da mai a matsayin makamashi, za su yi maraba da wannan faduwar farashi, domin kuwa zai saukaka masu. Ga kasashen da ke fitar da man fetur din kuwa, musamman kasashe masu tasowa, wannan faduwar farashi na nufin matsala a gare su, musamman ma kudin shigar su zai ragu, wanda haka na nufin kawo masu gibi ga kasafin kudi. Balle kuma a yadda ake hasashe, nan gaba kadan farashin zai kara sauka.
Najeriya na daya daga cikin kasashen da za su fuskanci matsala ta fuskar faduwar farashin nan, kasancewar tattalin arzikinta, kashi 90 cikin dari ya dogara ne da man fetur. Wannan kuwa ba karamin kalubale ba ne, ganin cewa sauran kudaden shiga na cikin gida, ba su taka kara sun karya ba. Ga kalubalen yaki da rashawa da cin hanci da satar dukiyar gwamnati, ga bukatar samar da ayyukan yi ga al’umma, ga batun yaki da talauci, ga batun gina ababen more rayuwa, ga kuma musamman matsalar yaki da ’yan ta’adda da ake ta faman yi, wanda ya jawo rashe-rashen rayuka da dukiya; ga kuma batun tallafa wa ’yan gudun hijira na cikin gida, wadanda suka tagayyara a sakamakon wadannan tashe-tashen hankali a Arewa.
Baya ga wadannan matsaloli, ga kuma batun cewa kashi 70 cikin dari na kasafin kudin kasar nan ana salwantar da shi ne ga harkokin da ba su kawo riba. Wani abin takaici ma, shi kansa kasafin kudin, ba a aiwatar da shi yadda ya kamata, domin da kyar ake aiwatar da kashi 35 cikin dari a kowace shekara. Wannan yanayi, al’amari ne mai kashe gwiwa game da gwamnati.
Tun a karshen shekarar 2013, masana harkokin tsimi da tanadai suka sanar wa gwamnati irin wannan hasashe, cewa zai iya faruwa; amma gwamnatin ba ta dauki matakin da ya dace don magance ko saukaka kaifin al’amarin ba. Maimakon haka sai jami’an gwamnatin suka ci gaba da harkar gabansu kawai, alhali al’amuran gwamnati na fuskantar barazana.
Masu tafiyar da harkokin arzikin kasa sun jaza wa gwamnati kamfar kudin shiga, kamar kuma yadda suka haifar da gurguncewar al’amuran ayyukan al’umma. A kwanaki ma, an gaza gudanar da taron nan da ake yi duk wata tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya don raba daunin dukiyar da kasa ta samu. An kasa gudanar da taron watan Oktoba 2014, saboda ganin cewa babu isassun kudi.
Akwai bukatar gwamnati ta maida hankali wajen tunkarar wannan kalubale, domin magance matsalolin da hakan kan haifar. Wani muhimmin abu kuma da ya kamata gwamnatin ta yi, shi ne ta waiwayi kasafin kudin 2014, don gyara shi ta yadda zai fuskanci 2015. Akwai bukatar yin haka, duk kuwa da cewa al’amuran zabe na karatowa.
Haka kuma ya zama wajibi gwamnati ta jajirce, ta dauki matakan da suka dace na lalabo wa kasar nan hanyoyin samun kudin shiga, ba kawai a dogara da hanya daya ta man fetur ba.