✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun bacewar mutane ya yi kamari

Kwamitin Majalisar dinkin Duniya Da Ke Bayar da Taimakon Gaggawa (The Internanational Committee of the Red Cross ICRC) ya ce kawo yanzu yana neman fiye…

Kwamitin Majalisar dinkin Duniya Da Ke Bayar da Taimakon Gaggawa (The Internanational Committee of the Red Cross ICRC) ya ce kawo yanzu yana neman fiye da mutum dubu 10 ne da suka bace a sassan duniya wanda ba a san halin da suke ciki ba.

Kwamitin ya yi wannan jawabi ne a ranar 30 ga watan Agsutan wannan shekara, watau ranar da Majalisar dinkin Duniya ta kebe don tunawa da mutanen da suke bacewa.  Majalisar ta kebe ranar ce don tunawa da mutanen da suke bacewa saboda yaki ko wadanda ake garkuwa da su ko wadanda bala’in ambaliya ko na girgizar kasa ko wadanda ke bacewa ta dalilin gudun hijira da kuma wadansu dalilai da dama.

Shugaban sashen da ke kula da kwamitin na bayar da jinkai a Najeriya Mista Eloi Fillion ne ya bayyana adadin mutanen da suka bace kawo yanzu a taron da ya gudana a Abuja.  Taron hadin gwiwa ne a tsakanin Majalisar dinkin Duniya da kuma Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta kasa (National Human Rights Commission, NHRC).

Shugaban ya kara da cewa, duk da rahotannin da ke nuna ana ci gaba da samun karuwar mutanen da ke bacewa, amma abin takaici hukumomi ba sa daukar matakan da suka dace don ganin an shawo kan al’amarin.

Ya ce Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (Red Cross) tare da hadin gwiwar Hukumar Kare Hakkin dan Adam yanzu haka suna binciken bacewar mutanen da yawansu ya kai dubu 10 da 480 kuma mafi yawa daga cikin wannan adadi yara ne.   Ya ce a wannan shekarar kadai sun samu sakonni daga wajen iyalai kimanin dubu 4 da ke neman bayani a kan bacewar ’yan uwansu da ba su san inda suke ko halin da suke ciki ba. Ya ce duk kokarin da iyalan suka yi don gano inda ’yan uwansu suke abin ya ci tura.

A Najeriya, yanzu haka mutanen da suka bace kuma aka nema ruwa a jallo sun haura dubu 10.  A kullum  ana samun bacewar mutanen da ba a san adadinsu ba.   Hasalima akwai mutanen da suka bace wanda ba a sanar da jami’an tsaro ba. Al’amarin bacewar ta fi kamari ne a karkara inda ba kasafai ne suke sanar da jami’an tsaro ba saboda tsoro ko kuma jahilci.

Mista Ellion ya kara da cewa kawo yanzu Hukumar ICRC ta gano mutane 746 inda tuni ta hada mutum 580 daga cikin wannan adadi ga iyalansu.  Ya ce hukumarsa tana goyon bayan yunkurin da hukumomi suke yi na daukar matakan gaggawa don shawo kan al’amarin bacewar al’umma.

Shugabar Hukumar Tattara Bayanan Mutanen da suka bace na Gwamnatin Tarayya Hajiya Maryam Uwais ta ce tuni gwamnati ta kammala shirye-shiryen daukar matakan gaggawa don ganin an shawo kan al’amarin bacewar mutane.  Ta ce za a fara gudanar da shirin kididdigar mutanen da suka bace ne a Jihohin Borno da Ribas da kuma Benuwai.  Ta ce shirin zai samar da sahihan bayanai ne a kan yawan mutanen da suka bace da wurin da ake ganin za a iya gano su da kuma samar wa iyalan wadanda suka bacen tallafi don a kwantar musu da hankali.

Batun yin tsafi da kuma garkuwa da mutane suna taka muhimmiyar rawa wajen bacewar al’umma, don haka muna maraba da wannan shiri na tattara bayanan mutanen da suke bacewa na gwamnati.  Sai dai akwai bukatar a fadada shirin zuwa sauran jihohin da ke fadin kasar nan.

Fiye da shekara 30 kenan da Najeriya ke yunkurin samar da cikakken bayanai a game da ’yan kasarta  amma abin ya ci tura.  Ya dace a karfafa batun yi wa ’yan kasa katin shaidar zama ’yan kasa (National ID Card)  inda za a dauki hotuna da cikakkun bayanansu da bayanan yatsunsu.  Hakan zai taimaka wa jami’an tsaro  wajen saurin gano wadanda suka bace cikin sauki.   Hakan zai bayar da damar da zarar an samu labarin bacewar wani ko wasu za a watsa batun a kafofin watsa labarai kuma zai taimaka wa jami’an tsaro wajen gano wanda ya bace cikin sauki.

Batun samar da kiddigar ’yan Najeriya yana da matukar muhimmanci tun da kasashen Nijar da Chadi da Kamaru da Ghana da Jamhuriyyar Benin sun samu nasara bayan sun aiwatar, don haka bai kamata a ce an bar kasar nan a baya ba.