Gwamnatin Jihar Sakkwato ta sanya dokar hana fita gaba daya bayan barkewar rikicin da ya biyo bayan kisan wata daliba da ake zargi da batanci ga Manzon Allah (SAW).
Tambuwal ya sanya da dokar hana fita ta awa 24 a Jihar Sakkwato ne domin dawo da zaman lafiya a birni da kewayen jihar.
- Batanci ga Annabi: Deborah ta wuce gona da iri —Farfesa Maqari
- Batanci: Tambuwal ya gana da malamai kan kisan Deborah
A safiyar Asabar ne aka tashi da zanga-zangar lumana domin neman a sako mutanen da aka kama da zargin sun kashe Daborah Yakubu kan ta yi batanci ga Manzon Allah (SAW).
Zanga-zangar lumana ta juya zuwa tashin hankali a wasu unguwanni abin da ya kai ga sanya dokar nan take.
Tun a ranar Juma’a Gwamnan Tambuwal ya yi zama da malaman Musulunci da jami’an tsaro a kokarin hana barkewar rikici kan batun batancin.