Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato ya tattauna da malaman Islama kan kisan dalibar nan da ta yi batanci ga Manzon Allah (SAW) a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke jihar, Deborah Samuel.
Tambuwal ya kira zaman da malaman da shugabannin hukumomin tsaro ne saboda dakile yiwuwar kai harin daukar fansa bayan kisan da aka yi wa Deborah kan zargin batancin.
- Batanci ga Annabi: Deborah ta wuce gona da iri —Farfesa Maqari
- Mako mai zuwa muke sa ran ASUU ta dawo aiki —Gwamnati
Gwamnan wanda ke neman takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP ya kira taron ne bayan ya soke ziyarar da ya shirya kaiwa domin zawarcin daliget da kusoshin jam’iyyar.
Ita dai dalibar ta gamu da gamu da karar kwana ne bayan ta furta lafuzan batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a kwalejin.
A kan haka ne fusatattun dalibai suka yi mata dirar mikiya suka kashe ta tare da banka wa gawarta wuta.
Lamarin ya jawo suka daga wasu kungiyoyi da shugabannin Musulunci, ciki har da Sarkin Musulmi, Muhammadu Abubakar.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato dai ta ce tana tsare da mutum biyu bisa zargin hannunsu a kisan Deborah, wanda ya tayar da kura a fadin Najeriya.