Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya janye dokar hana fita da ya sanya a birni da kewayen Jihar Sakkwato.
Janyewar wadda ta fara aiki nan take na zuwa ne a matsayin matakin da gwamnatin jihar ta dauka bayan tattaunawa da neman shawarwarin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
- Cutar kyandar biri ta bulla a kasar Kanada
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da wanda ya kai kudin fansar basarake a Kano
Gwamna Tambuwal ya gargadi mazauna jihar da suka kasance masu yi wa doka da’a sannan su zama jakadu na zaman lafiya a kowane lokaci.
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriyar ya jaddada muhimmancin hadin kai da zama cikin aminci a tsakanin al’ummar jihar.
Kazalika, ya haramta duk wata zanga-zanga a jihar har sai abin da hali yayi.
Gwamnan ya kuma mika godiyarsa ga al’ummar jihar dangane da hadin kan da suka bai wa dokar hana fita da aka sanya kwanaki kadan da suka gabata.
A safiyar Asabar ce wasu matasa suka soma wata zanga zanga wadda daga baya ta soma rikidewa zuwa tarzoma, abinda ya sa gwamnatin Jihar Sakkwato ta saka dokar hana fita ta tsawon sa’a 24.
Gwamnan ya sanya dokar ta-bacin ne domin shawo kan tashe-tashen hankula da suka biyo bayan kisan da aka yi wa wata dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da aka zarga da yin batanci ga Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SAW).