Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya ba da umarnin sassauta dokar hana fitan da gwamnati tana sanya a babban birnin Jihar kan batancin da aka yi wa Annabi Muhammad (S.A.W).
Gwamnan ya ce an dauki matakin ne bayan bayanin da jami’an tsaro suka yi masa kan ingantuwar harkokin tsaro.
Bisa ga wannan umarnin, yanzu an hana fitar ne daga faduwar rana zuwa wayewar gari a birnin Sakkwato da kewaye.
Gwamnatin ta ce an yi hakan ne domin a bai wa mutane dama su fita neman abinci da sauran sana’o’in su.
Kwamishinan Yada labarai na Jihar, Isah Bajini Galadanchi ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Sanarwar ta kuma shawarci jama’ar Jihar da su tabbatar da zaman lumana a tsakaninsu, tare da gargadin cewa ba za ta lamui duk wani nau’in taka doka da oda ba.
A makon da ya gabata ne gwamnati ta sanya dokar bayan wata zanga-zanga ta barke inda mutane ke neman ’yan sanda su saki mutanen da aka kama kan zargin kashe Deborah Samuel, wata dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar kan zargin zagin Annabi (S.A.W).