✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batanci ga Annabi: Kura ta fara lafawa a Sakkwato

Jami’an tsaro sun yi amfani da motoci wajen rufe manyan tituna

Sannu a hankali kura ta fara lafawa a Sakkwato bayan saka dokar hana fita a babban birnin Jihar sakamakon mummunar zanga-zangar da aka yi ranar Asabar kan batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W).

Masu zanga-zangar dai na neman ’yan sanda ne su gaggauta sako mutum biyun da suka kama bisa zarginsu da hannu a kisan Deborah Samuel, dalibar Kwalejin Shehu Shagari da ke Sakkwato, bisa zarginta da zagin Annabin.

Lokacin da wakilinmu ya zaga wasu daga cikin wuraren da ake fargabar barkewar rikici a cikinsu, ya iske yadda aka girke jami’an tsaro, wadanda ke kokarin tabbatar da an bi dokar hana fita ta awa 24 da Gwamnatin Jihar ta sanya ranar Asabar.

Wuraren sun hada da titin Emir Yahaya da Kanwuri (inda Fadar Sarkin Musulmi take) da titin Ahmadu Bello da kuma na Aliyu Jodi.

Sai dai ya lura cewa har yanzu shaguna da kasuwanni sun kasance a rufe, lamarin da ya hana mutane yin sayayyar bukatun yau da kullum.

Wani mazaunin birnin na Sakkwato ya shaida wa wakilin namu cewa jami’an tsaro sun je har yankin nasu, inda suka tilasta wa dukkan masu shaguna rufewa, sannan suka tilasta musu biyan tara.

Kazalika, wakilin namu ya lura da yadda jami’an tsaro suka yi amfani da motoci wajen rufe hanyoyi, yayin da suke kyale masu ayyuka na musamman kawai su wuce bayan tsattsauran bincike.

Sai dai yunkurin wakilin namu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar kan lamarin ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A wani labarin kuma, gwamnatin Jihar ta kara mako daya kan wa’adin komawa makarantun firamare da sakandire a Jihar.

A ka’ida dai za a sake bude makarantun ne ranar Litinin, 16 ga watan Mayun 2022, amma yanzu aka kara wa’adin sakamakon dokar hana fitar da aka saka.