✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Batanci: An kai wadanda ake zargi da kashe Deborah gidan yari

A ranar Litinin ’yan sanda suka gurfanar da daliban da ake zargi da kashe Deborah kan batanci ga Manzon Allah (SAW)

Kotu ta ba da umarnin tsare mutanen da ake zargi sun kashe dalibar nan, Deborah Yakubu, da ta yi batanci ga Manzon Allah (SAW) a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sakkwato, a gidan yari.

Kotun ta bayar da umarnin ne a ranar Litinin bayan ’yan sanda sun gurfanar da mutanen da ake zargi da kashe dalibar, wadanda su ma daliban kwalejin ne.

Daliban da aka gurfanar kan zargin su ne Bilyaminu Aliyu da kuma Aminu Hukunchi, wadanda kowannensu ya musanta laifin da ake tuhumar su da aikatawa.

A lokacin zaman kotun, ’yan sanda sun shaida mata cewa an gurfanar da daliban da ake zargi ne kan yi wa Deborah kisan gilla da daliban kwalejin suka aikata.

A kan haka ne dan sanda mai gabatar da kara, Isfekta Khalil Musa, ya bukaci kotun ta dage sauraron shari’ar domin su samu su karasa bincike.

Lauyan wadanda ake zargi, Farfesa Mansur Ibrahim, bai kalubalaci haka ba, amma ya nemi kotun ta ba da belin wadanda ake zargi, bisa tanadin 157, 161 (a,f) da kuma 164 na dokar manyan laifuka ta Jihar Sakkwato, had da sashe na 36(5) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.

Bayan nan ne kotun ta sa a kai su a tsare a Babban Gidan Yarin Sakkwato.

Alkalin ya ce nan gaba zai sanar da bangaren da ke kara ranar da za a ci gaba da sauraron shari’ar.

’Yan sanda sun shaida wa kotu cewa an gurfanar da daliban da ake zargi ne kan yi wa Deborah kisan gilla da daliban kwalejin suka aikata.