✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bata-gari sun tsarwatsa masu zabe a Kano

Aminiya ta kuma samu labari cewa kura ta lafa sanna aka ci gaba da zabe.

Al’amuran zabe sun tsaya cak bayan wasu bata-gari sun yi yunkurin fasa akwatinan zabe tare da saran wasu mutane a rumfar zaben da ke Makarantar Firamaren Kadawa a Karamar Hukumar Ungogo, Jihar Kano.

Wata mata da lamarin ya faru a kan idanunta mai suna Fatima Alu ta ce suna kan layin zabe sai suka ga bata-garin samarin sun fito da adduna suka fara sarar mutanen da ke wurin.

“Muna zaune a layi sai wasu matasa suka zo wurin suka fito da adduna suka farfasa akwatinan suka kuma sari wani mutum akansa.”

Matar ta bayyana cewa  hakan ya sa mutane tserewa suka bar wurin don gudun abin da ka iya faruwa.

Sai dai wasu rahotanni da Aminiya ta samu sun bayyana cewa bayan da jami’an tsaro suka zo wurin sun je har gida sun kama wadanda suka tayar da rigimar tare da wanda ya turo su.

Aminiya ta kuma samu labari cewa kura ta lafa sanna aka ci gaba da zabe.