Al’amuran zabe sun tsaya cak bayan wasu bata-gari sun yi yunkurin fasa akwatinan zabe tare da saran wasu mutane a rumfar zaben da ke Makarantar Firamaren Kadawa a Karamar Hukumar Ungogo, Jihar Kano.
Wata mata da lamarin ya faru a kan idanunta mai suna Fatima Alu ta ce suna kan layin zabe sai suka ga bata-garin samarin sun fito da adduna suka fara sarar mutanen da ke wurin.
Matar ta bayyana cewa hakan ya sa mutane tserewa suka bar wurin don gudun abin da ka iya faruwa.
Sai dai wasu rahotanni da Aminiya ta samu sun bayyana cewa bayan da jami’an tsaro suka zo wurin sun je har gida sun kama wadanda suka tayar da rigimar tare da wanda ya turo su.
Aminiya ta kuma samu labari cewa kura ta lafa sanna aka ci gaba da zabe.