✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bata gari sun kone caji ofis sun sace makamai

Maharan sun fasa dakin ajiyar makamai a harin da suka kai da tsakar dare.

’Yan daba sun kai hari a ofishin ’yan sanda inda suka fasa rumbun makamai suka yi awon gaba da su bayan sun kashe wani hafsan dan sanda sannan suka banka wa caji ofis din wuta.

Kakakin ’yan sandan Jihar Abiya, Geoffrey Ogbonna ya ce da misalin karfe 3 na dare ne maharan suka kai hari a caji ofis din inda suka kashe wani hafsan dan sanda mai mukamin Insfekta, suka kuma jikkata wata ’yar sanda.

Ya bayyana cewa a lokacin harin caji ofis din Umuoba dake a Karamar Hukumar Isiala Ngwa ta Arewa a Jihar, “Miyagun sun fasa rumbun makamai suka sace bindigogi ciki har da ta Insifektan da suka kashe.

“Sun kone caji ofis din tare da motar sintiri da aka aijye a farfajiyar ofishin.

“An dauke gawar jami’in dan sandan da ya rasu, ’yar sandar da suka ji wa rauni kuma an kai ta asibiti, inda aka yi mata magani,” inji Ogbonna.

Ya kara da cewa tuni ’yan sanda a jihar suka baza komarsu don gano maboyar maharan.

Ogbonna ya ja hankalin jama’ar jihar da su sanya idanu kan duk wanda ba su yarda da take-takensa ba.

Har wa yau, ya roki masu otal-otal a fadin jihar da su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri a kan duk wanda suke zargi da hannu a cikin lamarin.

Rundunar ’yan sandan jihar, ta yi alkawarin adana bayanan duk wanda ya taimaka wajen cafke wanda suka aikata laifin.