✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bata-gari sun fasa shagon Mansura Isah a Kano

Na shiga damuwa ganin halin da na samun sabon shagon nawa.

Masura Isa, tsohuwar tauraruwar finan-fina Hausa ta tafka asara bayan bata-gari sun fasa shagonta sun kwashe komai a tarzomar zanga-zangar #EndSARS a garin Kano.

Mansura Isah, wargida ga tauraro kuma mawaki a masana’antar Kannywood, Sani Musa Danja na daga cikin mutanen da bata-gari basu barta ba.

Tsohuwar jarumar ta wallafa bidiyo da hotunan shagon da aka fasa mata a shafinta na Instagram.

“Mun kwashe kayanmu a sauran ofisoshinmu da ke unguwar Badawa zuwa wuri daya domin rage wa kanmu damuwa.

“Mun kwashe komai da ke shagon: takalma, firji, talabin da sauran kayayyaki.

“Dama mun san mutane suna neman irnin wannan dama domin aikata mummunan laifi — Sun fake da zanga-zangar #EndSARS da #EndInsecurity sun cimma mummunan kudirinsu”, a cewar Mansura.

Bata-garin sun fasa shagon nata da ke kan titin Filin Jirgin Sama daura da titin Ahmadiyya, inda suka hajoji ta kuma da kaayn laturoni da ke shagon.

Mansura yayin duba barnar da aka yi sa shagonta

Yayin tattaunawarta da Aminiya, tsohuwar jarumar, wadda a yanzu ta fi maida hankali wajen tallafawa rayuwar marasa karfi, ta bayyana cewa ta shiga damuwa ganin halin da ta samun sabon shagon nata.

Mansura Isah a bakin kofar shagonta da aka fasa aka kwashe kaya.

Mansura ta ce ta fallawa Allah asarar da ta yi kuma ta dauki lamarin a matsayin kaddara.

Ta kara da cewa suna fatan samun canji da zaman lafiya a Najeriya, sannan ta gode wa Allah da ya ba mu lafiya da rayuwar zama lafiya.