Wasu fusatattun matasa a yankin Igboukwu na karamar hukumar Aguata ta jihar Anambra sun kone ofishin ‘yan sandan yankin bayan jami’an ‘yan sanda sun harbe wani dan acaba har lahira a garin.
Aminiya ta gano cewa lamarin ya biyo bayan samun takun-saka tsakanin jami’an da ‘yan acaba biyo bayan kwace musu baburan da aka yi saboda karya dokar hana zirga-zirga a jihar wacce ke fara aiki tun daga karfe tara na dare.
- Kwale-kwale ya kife da ’yan sanda 3 a jihar Ribas
- Janar din sojojin Najeriya 18 sun kamu da COVID-19
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, SP Haruna Mohammed ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewar sa, lamarin ya rikide zuwa tarzoma da kuma jikkata wani dan acaba tare da kona ofishin jami’an su dake Igboukwu da wasu fusatattun matasa suka yi.
A wani labarin kuma, Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP John Abang ya yi kira da a kwantar da hankula tare da ba da umarnin zakulowa da kuma hukunta jami’an da suke da hannu a ciki.
Haruna ya ce, “Kwamishinan ya kuma yi Allah-wadai da lamarin tare da ba da umarnin yin zuzzurfan bincike a kai.
“Kazalika, ya tabbatar wa jama’a cewa za su tabbatar an yi adalci a binciken, wanda kuma zai gudana a bainar jama’a,” inji Kakakin.