Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya nemi Majalisar Dattawa da ta dakatar da bai wa Shugaban Muhammadu Buhari duk wata dama ta karbo bashi a nan gaba.
Atiku ya aike da wasika ga Shugaban Majalisar, Sanata Ahmed Lawan, inda ya bukaci a jingine bai wa Shugaban Kasar damar sake karbo bashin da a cewarsa ba ya tsinana wa kasar komai.
- Allah Ya yi wa surukar Atiku rasuwa
- Yadda ‘yan kasar waje ke juya farashin fulawa a Najeriya
- An kara farashin wutar lantarki a Najeriya
A wasikarsa mai dauke da kwanan watan ranar 25 ga Agusta, Atiku ya yi kira ga ’yan Majalisar Dattawan da su tsagaita bai wa Shugaba Buhari damar karbo bashin da babu wata riba da kasar za ta samu a cikinsa.
Wazirin Adamawa ya ce Najeriya za ta iya shiga tsaka mai wuya muddin aka ci gaba da karbo basussuka duba da wadanda aka karba a baya ba su haifar wa kasar wani da mai ido ba.
A kididdigar da Ofishin Kula da Basussuka na Najeriya (DMO) ya fitar a watanni biyu da suka gabata, ya nuna cewa a rubu’in farko na bana, bashin da ya yi wa kasar kanta ya kai Dala miliyan 79.3.