Ministan Sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi da Shugaban Ofishin kula da bashi (DMO) da kuma jami’an ma’aikatar kudi sun gurfana gaban Kwamitin Majalisar Wakilai domin su yi bayani kan bashin da Najeriya za ta karba daga Gwamnatin China da sauran kasashe.
Kwamitin da Ossai Nicholas Ossai (PDP, Delta) ke jagoranta, ya nemi kowannensu ya bayyana rawar da ya taka a yarjejeniyar kwangilolin da aka bayar.
Idan ba a manta ba, kwamitin a zamansa na baya ya ce yarjejeniyar bashin ka iya sa Gwamnatin China ta mayar da Najeriya baiwarta.
Shi kuma Amaechi ya roki kwamitin ya daina binciken kan bashin kar ya jawo China ta fasa bayarwa.
Amaechi ya ce, rasa bashin da China za ta bayar na iya tsayar da manyan ayyukan da Gwamnatin Tarayya take gudanarwa.
Ba bashin China kadai muke bincike ba —Ossai
Da yake bude taron, Ossai ya ce an gayyace su Amaechi ne domin kara dubar yarjejeniyar karbar bashin da kuma kwangilolin ma’aikatun gwamnati.
Ya ce, kwamitin ba wai ya mayar da hankali ne kawai ga bashi ko kwangilolin da China za ta ba Najeriya ba, har ma da sauran basusuka da ba na China ba.
“Kamar yadda muka sani, Najeriya tana da fiye da yarjejeniya 500 ta basusuka da kwangiloli daga kasashen waje. Tana kuma da yarjejeniyar kasuwanci da kasashe daban-daban
Babu yadda za a yi kwamitin ya gudanar da binciken sai ya rarraba aikin zuwa kasa-kasa ko ma’aikata-ma’aikata. Don haka ba wai saboda China ake binciken ba, kuma ba muna yi ba ne don hana ayyukan jigin kasa ci gaba”, inji shi.
Ossai ya ce, yarjejeniyar bashin da ya gani ta yi nuni da cewar jami’an gwamnati da aka wakilta su shiga tsakani sun kagara su karbi bashin ba tare da bin abun daki-daki ba kuma ba tare taka tsantsan kan abun da ka iya biyowa baya ba.