Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya yaba wa Babban Bankin Najeriya (CBN) bisa kirkiro da ba da rance mara ruwa ga manoma da sauran masu kananan sana’o’i.
Ya bayyana haka ne ranar Alhamis lokacin da yake tsokaci kan rahoton jaridar Daily Trust cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA), Farfes Salisu Shehu ya sanya wa hannu a Sokoto.
Sarkin Musulmi wanda shi ne shugaban Majalisar ya ce kudin ruwa ya dade yana dakushe masu kanana da matsaskaitan sana’o’i a Najeriya, yana mai cewa hakan na taka muhimmiyar rawa wajen kara ta’azzarar talauci a tsakaninsu.
Ya kuma yi kira ga CBN da ya bi duk hanyoyin da suka kamata kamar Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) da sauran kafafen yada labarai na rediyo da talbijin wajen fadakar da mutane kan hanyoyin cin gajiyar rancen.
A cewarsa, shirin zai kawo karshen wariyar da ake yi wa Musulman Najeriya a harkokin kudin kasar saboda kudin ruwan da ke a cikin mafi yawan tallafin, wanda hakan ke dakile su a lokuta da dama.
“Ga mu Musulmai da mu ne fiye da rabin ‘yan kasar nan, mun dade muna kaffa-kaffa da batun kudin ruwa matuka, kuma na san yawancin Musulmi sun gwammace su zauna a talauci da su karbi bashi mai ruwa saboda gudun fishin Mahaliccinsu”, inji sarkin.
Ya kara da cewa, “Rashin samar da bashi mara ruwan ya tilasta mayar da kusan kaso 60 cikin 100 na Musulmai saniyar ware, ya kuma kara yawan talauci a tsakaninsu.
“Rashin bashi mara ruwa zai hana CBN cimma muradunsa na ganin cewa kaso 80 cikin 100 na ‘yan Najeriya sun fita daga kangin talauci ko kuma samun wani cigaban tattalin arziki mai ma’ana nan da wani dan lokaci”, inji shi.