Magajin Garin Jama’a, Alhaji Abubakar Muhammad Isa ya shawarci dalibai su guji tu’ammali da miyagun kwayoyi kuma su zamo nagari masu kyawawan halaye tare da zage damtse wajen ci gaba da neman ilimi domin samun nasara a fagen ilimi da kasuwanci da shugabanci sannan su zamo jakadu nagari da za a yi alfahari da su nan gaba.
Alhaji Abubakar Muhammad Isa ya bayyana haka ne a wajen bikin yaye daliban da suka kammala karatun firamare a makarantar Ma’aji Memorial Islamic School da ke garin Kafanchan a Jihar Kaduna, inda ya ce, “Ina kara yin kira gare ku da ku yi watsi da munanan halaye da suka hada da shan miyagun kwayoyi da satar jarrabawa a manyan makarantu, kuma ku guji zaman banza da ha’inci da almundahana. Ku zamo wadanda za su kawo gagarumin sauyi a masarautar Jama’a da duniya baki daya.”
Magajin Garin ya ce yana matukar alfahari da makarantar domin nan ne tushen samun ilimi da tarbiyyar da ya samu har zuwa lokacin da ya kammala a shekarar 2006, inda ga shi yau ya kammala karatun digirinsa na farko a Jami’ar Amurka ta Najeriya cikin nasara.
Ya bayyana ilimin firamare a matsayin tubali na farko da ake fara kintsa tarbiyyar yara da kuma shirya su don ba su damar fuskantar kalubalen rayuwa. Ya ce hakan ya sa kungiyoyi da yawa na gwamnati da masu zaman kansu da kasashe suke bai wa ilimin firamare fiffiko don cimma nasara.
Tunda farko a jawabin, Malam Aliyu Abbas Jama’a ya yi jinjina ne ga malaman makarantar kan namijin kokarin da suke nunawa wajen sa makarantar ta tsayu da kafafunta sannan ya yi kira ga daliban da suka kammala firamare su sani cewa yanzu ne suka sa dan ba wajen neman ilimi inda ya yi kira ga mahalarta taron su rika sanya Musulunci a dukan harkokinsu na rayuwa.
A karshe an raba kyaututtuka ga daliban da aka yaye bayan sun kayatar da mahalarta taron da wasan kwaikwayo da jawabai cikin harshen Ingilishi da Larabci.