Dagacin Na’ibawa a Karamar Hukumar Kumbotso, Jihar Kano, Ibrahim Yusuf, ya yi alkawarin mara wa shirin hana bahaya a fili baya don cimma manufarsa ya zuwa 2025.
Basaraken ya sha alwashin ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin kula da tsafta na kasa da aka fi sani da NTGS a takaice ranar Litinin.
- Mahara sun kashe mutum 2 sun sace 13 a Sakkwato
- Uba ya karya hannun jaririnsa mai wata 2 saboda kuka
Kwamitin ya kai ziyarar yankin ne don bin diddigin yadda ayyukansa ke gudana a wasu kauyukan yankin.
Idan dai za a iya tunawa, a lokutan baya Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da wani shirin yaki da yin ba-haya a fili da nufin kawar da natsalar baki daya ya zuwa 2025.
Yusuf ya ce zai ba da gudunmawar tasa ne ta hanyar karfafa wa jama’arsa kan sha’anin kula da tsafta a gida da waje, kamar rungumar dabi’ar wanke hannu da sauransu.
Ya ce, a halin da ake ciki babu gidan da babu masai a yankinsu albarkacin wannan shirin.
(NAN)