Barkwanci wani salon magana ne da Allah kan huwace shi ga daidaikun mutane, ta yadda za su kasance masu fasaha a duk zancensu, hakan ya sa da zarar sun yi magana sai an yi raha; akalla a yi murmushi. Barkwanci na iya zama tsararren zance na ban-dariya, musamman wanda aka shirya shi don zolaya ko tsokana.
A wani fannin kuma, barkwanci shi ne irin wasannin da ke tsakanin kabilu ko al’umma, ta dalilin aukuwar wani lamari mai girma a tsakaninsu. Haka kuma, wasan da ake samu a tsakanin taubasai (abokan wasa na dangi) ana kiransa barkwanci.
Kamar yadda masana suka hadu a kai, akwai dalilai iri-iri da suke haifar da barkwanci a cikin al’umma. Mafi yawanci dai yake-yaken da suka auku tun da dadewa suna a sahun farko na assasa barkwanci – wasannin da ke tsakanin kabilar Fulani da Barebare (Kanuri) da tsakanin garuruwan Kano da Zariya; Kano da Damagaram da kuma Katsinawa da Nufawa, duk misalai ne na barkwancin da yaki ne musababinsa. Wasu dalilan da ke haifar da barkwanci sun hada da zaman tare, musamman ga masu sana’a a wuri daya – kamar direbobi da ’yan kamasho, kwambalar wasannin gargajiya kamar dambe da kokowa da shadi da makamantansu da ke wakana a tsakanin garuruwa makwabta wani dalili ne da kan samar da barkwanci; zumunci, misali tsakanin taubasai da tsakanin kabilar Fulani da Tibi na daga cikin abin da ke haifar da barkwanci.
Wai an ce zaman tare ya hada wani Bafulatani da dan kabilar Tibi. Da Bafulatanin nan zai yi tafiya sai ya ba Tibin amanar duk kadararsa, suka yi ban-kwana. Kafin Bafulatani ya dawo Tibi ya hau kan kayan duk ya cinye, bai rage komai ba. Bafulatani na dawowa ya tambayi Tibi game da ajiyarsa, sai ya budi baki ya ce: “Mun ci!” A wata ruwayar kuma wai Bafulatanin nan amanar matarsa ce ya bar wa Tibi, ko da ya dawo sai ya iske ta da ciki. Yana tambayar me ke faruwa haka, sai Tibi ya ce: “Mun ci!” Wannan dalili ne ya sa har gobe za a ji Fulani na kiran Tibi da sunan “Mun ci.”
Wannan misalin nau’in barkwanci ne shiryayye da ke tsakanin kabilar Fulani da Tibi.
Barkwanci ba na yaku-bayi ba ne kadai, hatta sarakai da ma’aikatan gwamnati na yin sa. Ba zan manta ba, a zamanin Sarkin Katsina, marigayi Alhaji Kabir Usman na ga wani shiri da gidan talabijin na Jihar Katsina ya hasko shi kai-tsaye. Sarkin na tafiya a cikin wata babbar motar safa, tare da shi akwai wadansu sarakuna da hakimai da dogarai. A nan na ji suna ta barkwanci a tsakaninsa da wani basarake (saboda karancin shekaru a lokacin na manta wane basarake ne, amma ina zaton Banufe ne ko Bagobiri). Haka ma a kusa-kusan nan na samu labarin barkwancin da ya wakana a fadar Sarkin Katsina. An rawaito cewa, taron aure ne ya hada Sarkin Katsina da wani kwamishina da ya zo daga Jihar Neja, inda Sarkin ya murtuke, ya kalli wannan kwamishina ya ce: “Duk jami’in da ya zo daga Jihar Neja kada a bar shi ya fita, a daure shi.” Mutane suka fara kallon-kallo. Da Mai martaba ya lura, sai ya saki fuska ya ce: “Saboda su bayinmu ne.” Nan fa raha ta dawo sabuwa a fada, musamman ga mutanen da suka san wannan tada ta barkwanci.
Makada da mawaka su ma sukan sa barkwanci a cikin wakokinsu. A wakar marigayi Musa Dankwairo ta Shehun Borno an samu sofanen barkwanci a cikinta, inda yake cewa:
“Ina ta kidin Shehun Borno, Hilani duka sun yi shiru. Kidin manyansu nis shiryo.” Da kuma wani baiti dai can gaba a cikin wakar,
“Dauki sansanin yaki ka fito, ka jawo baraden yaki, kar ka tsaya sai ga ka ga Bauchi. Tun da tamburanka na Bauchi, a wajjen Yakubun Bauchi. Ka ji ana ta kidi suna kara…”
Haka kuma a wani taro na murnar cikar Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna shekara hamsin da kafuwa, na ji mawaki Dokta Dan Maraya Jos ya yi wani barkwanci mai kama jiki. An ba shi fili ne wajen taron, ga Zage-Zagi cunkushe, ga kuma Gwamnan Kanawa, Injiniya Rabi’u Kwankwaso, sai da ya zo karshen wakar, sai ya ja wani baiti:
“In har Kwankwaso ka cika Gwamnan Kano, ina son kai min wata kyauta!”
Sai da ya maimaita baitin cikin salo daban-daban kusan sau uku, fili duk ya yi tsit, wadansu na ganin ya zub da dattakonsa in dai har zai yi roko irin wannan kai-tsaye ga wani, kuma a taro irin wannan, can sai ya karashe da cewa:
“In dai har ka cika Gwamnan Kanawa, kai min kyauta da Bazazzagi!” Nan wuri kowa ya goce da sowa, ba wanda bai dara ba.
Barkwanci dai tada ce mai dogon tarihi, ana zaton ta faro ne bayan karkare jihadin da Shehu Usmanu ya jagoranta a yankin Hausa. Wannan tada na karfafa zumunci da sa juriya ko karfin zuciyar shanye duk wata magana ga mazauna wuri daya; tana saka nishadi da raha ga ma’abota rikonta; ta zama taskar adana tarihi. Kai a takaice dai tana kimshe da fa’idoji masu yawa, wadanda zurfafa nazari da tunani kadai zai fito da su.
Da haka nake kira ga duk masu ruwa-da-tsaki kan raya tadodin Hausawa da sauran kabilu kan su mike tsaye domin farfado da wannan al’ada ta Barkwanci ga al’umma.
Za a iya tuntubar Malam Hafiz ta adireshinsa na I-mel [email protected]