An yi jana’izar tsohon Shugaban Kungiyar Kasashe Masu Arzikin man Fetur ta Duniya (OPEC), Muhammad Sanusi Barkindo, a Yola, babban binin Jihar Adamawa da yammacin Laraba.
Marigayin, wanda ya rasu ranar Talata a Abuja dai an binne shi ne a makabartar Damare da ke birnin na Yola.
- Barkindo: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da tsohon Babban Sakataren OPEC
- PDP ta zabi ’yar wasan kwaikwayo a takarar Mataimakiyar Gwamnan Legas
Daruruwan abokai da ’yan uwan marigayin ne suka yi dafifi a filin jirgin saman Yola da misalin karfe 12:30 na ranar Laraba, domin tarbar gawar marigayin cikin yanayin alhini.
An dai yi masa sallar jana’iza ne a babban masallacin Yola na Modibbo Adama wanda ke Fadar Lamidon Adamawa da misalin karfe 4:00 na yamma.
Jana’izar dai ta sami halartar manyan baki daga Najeriya da kuma kasar Kamaru.
Daga cikin wadanda suka sami halartar jana’izar akwai Ministan Abuja, Muhammad Musa Bello, da na Sufuri, Muazu Sambo Jaji, da Sakataren Gwamnatin Jihar Adamawa, Bashiru Ahmad da kuma Lamidon Adamawa, Dokta Barkindo Aliyu Mustapha.
Wani dan uwan marigayin, Abduljalal Barkindo, ya ce tsohon Shugaban na OPEC ya rasu ya bar mata biyu da da daya sai kuma ’yan uwa su takwas.