Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Josep Maria Bartomeu, zai shaida wa dan wasan Argentina Lionel Messi, shirin da kungiyar ta ke yi na rage albashinsa.
Cikin wani rahoto da jaridar Departos Cuatro ta kasar Spaniya ta wallafa, ya ce dan wasan ba ya da wani katabus a wannan karo face sai ya yi ido biyu da shugaban kungiyar kan batun albashinsa.
Bayan mayar masa ta mukamin jagoranci na Kyaftin a kungiyar, dole ne dan wasan ya jagoranci sauran ‘yan wasanta domin sanin inda aka dosa game da batun albashinsu duba da matsalar tattalin arziki da annobar Covid-19 ta haddasa.
Alkaluma sun nuna cewa kungiyar ta yi asarar kusan Yuro miliyan 98 ya zuwa lokacin da aka kammala gasar La Liga ta zangon 2019/2020.
A ranar 25 ga watan Agusta ne dan wasan mai shekaru 33, ya mika wa Barcelona takardar sakinsa saboda bakin cikin rashin nasarar da ta yi a kakar wasanni da aka karkare.
Sai dai dole ‘kanwar naki’ ta sa dan wasan zai ci gaba da zama a Barcelona sakamakon ba zai yiwu wata kungiya ta iya biyan farashin Yuro miliyan 700 da kungiyar ta nema a kansa ba.