Barcelona za ta buga wasannin sada zumunta hudu a Amurka, ciki har da kece raini da za ta yi da Real Madrid da Juventus a shirye-shiryen tunkarar kakar badi ta tamaula.
Barcelona za ta fafata da Real Marid a ranar 23 ga watan Yuli a Las Vegas, sannan bayan kwana uku ta fafata da Juventus a Dallas.
- ‘Matsafa na bin makabartu su hako gawarwakin ’yan uwanmu’
- NAJERIYA A YAU: Shekara 23 Da Mulkin Dimokuradiyya: Ina Aka Kwana?
Kungiyar Camp Nou za ta fara wasan sada zumunta da Inter Miami ranar 19 ga watan Yuli, wasa na hudu kuwa za ta yi ne da New York Red Bulls aranar 30 ga watan Yuli.
Wasan da Barcelona za ta yi da Real Madrid, shi ne El Clasico na biyu da za su kara a Amurka.
Sun fara karawa cikin Yulin 2017 a filin wasa na Hard Rock a gaban ’yan kallo 54,000.
Wannan karon za su fafata a filin wasa Allegiant, mai cin ’yan kallo 65,000, kuma karon farko da Barca za ta yi wasa a Las Vegas.
Idan Barca ta buga da Real Madrid, sai ta fuskanci Juventus ranar 26 ga watan Yuli a Cotton Bowl a Dallas, filin da ke daukar ’yan kallo 92,100.