✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Barcelona za ta iya sallamar kocinta, Koeman

Barcelona ta fice daga jerin kungiyoyin da za su iya lashe gasar Laliga a bana.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fice daga jerin kungiyoyin da za su iya kashe gasar Laliga ta bana, bayan kashin da ta sha a hannun Celta Vigo da ci 1-2 a ranar Lahadi.

Ronald Koeman, ya ci gaba da shan suka daga magoya bayan Barcelona da masu sharhi kan wasanni kan yadda yake tafiyar da kungiyar.

Wasu na ganin ba lallai Kocin Barcelona ya iya kai kungiyar wani mataki ba, musamman duba da yadda take samun koma baya a wasannin da take bugawa.

A baya-bayan nan Celta Vigo da Granada dun doke Barcelona, sannan ta ci kunnen doki da Athletico Madrid da kuma Levante, wanda hakan ya sa ta ci kasa a gasar Laliga a bana.

Shi kansa, Koeman ya sha fadin cewar ba lallai ya ci gaba horar da Barcelona ba, ganin yadda al’amura suka kasance masa.

Ko a baya-bayan nan, yayin da ya tattauna wa da MARCA, ya bayyana cewar “ba ni da tabbas game da makomata a Barcelona”.

Makomar tasa ta ta’allaka ne a hannun shugaban kungiyar, Laporta, wanda ya gana da Koeman a ranar Alhamis da ta gabata don jin ba’asin rashin yin nasara da kungiyar ta yi a wasanta da Levante.

Rahotannin daga kasar Spain na nuni da cewar in har kungiyar ta sallami Koeman, akwai yiwuwar a ba wa tsohon kaftin dinta, Xavi Hernandez, ragamar horas da ita.