✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Barcelona za ta dauko Aguero, Chelsea na son Dembele, Ahmed Musa zai fara karbar horo a West Brom

Mai horas da ’yan wasa a kungiyar Leicester City, Brendan Rodgers, na daya daga cikin wadanda Chelsea take son kawowa kungiyar a yayin da kocinta…

Mai horas da ’yan wasa a kungiyar Leicester City, Brendan Rodgers, na daya daga cikin wadanda Chelsea take son kawowa kungiyar a yayin da kocinta Frank Lampard ya gaza tabuka wani abun a yaba a kungiyar a kakar wasannin Firimiyar Ingila ta bana. Daily Star

Da yiwuwar Manchester United za ta bayar da aron dan wasanta na Kasar Ingila, Jesse Lingard mai shekaru 28 bayan karawar da za ta yi da Liverpool a gasar Kofin FA. Ana sa ran daya daga cikin kungiyoyin Newcastle, Sheffield United da West Brom ce za ta karbi dan wasan aro duba da yadda kowannensu ya nuna sha’awarsa. Mail

Barcelona ta kulla aniyyar dauko dan wasan Manchester City na kasar Argentina, Sergio Aguero da dan wasan Bayern Munich na kasar Australia David Alaba, a bazara idan kwantaragin kowannesu ya kare. Mundo Deportivo.

Real Madrid ta karkata wajen dauko dan wasan Borussia Dortmund mai shekara 20 dan kasar Norway, Erling Braut Haaland, wanda Manchester da Chelsea sun nuna sha’awarsu a kai bayan dan wasan PSG na Kasar Faransa Kylian Mbappe mai shekara 22 ya zille musu. Express

Chelsea ta ki amincewa da tayin West Ham na karbar aron dan wasanta na Kasar Italiya, Emerson Palmieri mai shekaru 26. Sunday Mirror

Leicester City da Everton sun nuna sha’awarsu ta dauko dan wasan Southampton na Kasar Ingila, Danny Ings, a yayin da ya rage saura watanni 18 kwantaraginsa ya kare. 90 Min

Manchester United da Chelsea sun fara lura da halin dan wasan Barcelona na Kasar Faransa, Ousmane Dembele, a yayin da watanni 18 kacal suka rage kwantaraginsa ya kare. Sport via Metro

Bayan barin kungiyar Dalian Professional ta Kasar China, tsohon Kocin Liverpool da Newcastle United Rafael Benitez, ya nuna sha’awar komawa fagen horas da ’yan kwallo cikin gaggawa, inda rahotannu suka nuna cewa Napoli da Roma na zawarcinsa. Sunday Times.

Manchester United da Liverpool sun fara sanya idanun lura a kan dan wasan Ingila mai shekeru 17 Jamal Musiala wanda ke buga kwallo a rukunin ’yan kasa da shekara 21. Goal

Real Madrid ta fara shirin mika tayin fam miliyan 45 domin sake sayo dan wasanta mai tsaron baya Sergio Reguilon daga Tottenham. Sport

Porto ta kammala shirin mika tayin dala miliyan 12 domin sayen dan wasan tsakiya na Manchester United Jesse Lingard, a cewar Todofichajes.

Mesut Ozil ya ce zai ci gaba da kasancewa dan wasan Arsenal har abada bayan ya koma kungiyar Fenerbahce ta kasar Turkiyya a ranar Lahadi.

Dan wasan ya ce dankon zumuncin da ke tsakaninsa da Arsenal ba zai taba yankewa ba duk ya bar kungiyar bayan kunsan shekaru takwas ana tare. Goal

Lucas Vazquez ya yi watsi da tayin tsawaita kwantaraginsa wanda kungiyar Real Madrid ta gabatar masa a cewar jaridar Cadenas SER.

Rahotanni sun nuna cewa an gabatar wa da dan wasan yarjejeniyar tsawaita kwaraginsa zuwa shekaru uku masu zuwa a kan albashin da aka saba biyansa sai dai dan wasan ya nuna bukatar kari a kan hakan.

Tsohon dan wasan Leicester City dan Kasar Najeriya Ahmed Musa zai fara karbar horo a West Brom cikin wannan mako a cewar The Telegraph yayin da kungiyar ta kuma kyalla idanunta a kan dan wasan gaba na Galatasaray Mbaye Diagne. Express

West Brom ta fara shirin mika tayin dan wasan gaba na Crystal Palace, Christian Benteke a cewar Express and Star