✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona ta shiga zawarcin Messi

Ya bar Camp Nou a 2021, bayan da kungiyar ta fada matsin tattalin arrziki.

Barcelona ta tuntubi Lionel Messi kan batun sake komawa Camp Nou, in ji mataimakin shugaba, Rafael Yuste.

Mai shekara 35, shi ne kan gaba a ci wa Barcelona kwallaye a tarihi, mai 672 a raga a wasa 778.

Ya bar Camp Nou a 2021, bayan da kungiyar ta fada matsin tattalin arrziki.

A karshen kakar nan yarjejeniyar shekara biyu da ya kulla a Paris St Germain za ta cika, wanda ake hasashen yana son ci gaba da taka leda a Faransa.

Tun farko Messi ya amince da kunshin kwantiragin da Barca ta gabatar masa har da rage albashi kaka biyu da ta wuce, amma aka sayar da shi, bayan da kungiyar ke neman kudi ruwa a jallo.

Hakan ya sa ya hakura da kungiyar da ya lashe Champions League hudu da La Liga 10 da Ballon d’Or shida.

Messi wanda ya dauki Kofin Duniya a tawagar Argentina a Disambar 2022 a Qatar, ya ci kwallo 29 a wasa 66 a PSG.

Kwanan nan ya ci kwallo na fiye da 100 a tawagar Argentina da kuma na sama da 800 a tarihinsa na murza leda.