✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Barcelona ta sayi Jules Koundé daga Sevilla

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta cim ma yarjejeniya da takwararta ta Sevilla don dauko dan wasan bayanta, Jules Koundé, a kan kudi sama da…

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta cim ma yarjejeniya da takwararta ta Sevilla don dauko dan wasan bayanta, Jules Koundé, a kan kudi sama da Fam miliyan 50.

A makon da ya gabata ne rahotanni suka bayyana yadda dan wasan ya gama cim ma matsaya da kungiyar ta Barcelona.

A baya dai kungiyar Chelsea ta kasar Ingila ta yi kokarin daukar dan wasan a kan kudi Fam miliyan 55 kamar yadda rohatanni suka nuna.

Sai dai dan wasan ya nuna bai da ra’ayin taka leda a kasar ta Ingila.

Wannan dai shi ne kusan karo na uku da Barcelona ke kasa kungiyar Chelsea a wajen sayen ’yan wasa, na baya-bayan nan dai shi ne dan wasan gaban Leeds United dan asalin kasar Brazil wato Raphinha da Barcelona din ta siya a lokacin da Chelsea ke dab da daukarsa.

Hakazalika shi ne dan wasa kusan na biyar da Xavi ya siyo a kakar wasar bana, a wani yunkuri na ganin ya dawo da martabar kungiyar ta Barcelona a idon duniya.