Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta cim ma yarjejeniya da takwararta ta Sevilla don dauko dan wasan bayanta, Jules Koundé, a kan kudi sama da Fam miliyan 50.
A makon da ya gabata ne rahotanni suka bayyana yadda dan wasan ya gama cim ma matsaya da kungiyar ta Barcelona.
- Majalisa ta yi sammacin Emefiele bayan canjin Dala ya kai N700
- Buhari yaba da umarnin fito da jirage don fara sufuri a kamfanin Nigerian Air
A baya dai kungiyar Chelsea ta kasar Ingila ta yi kokarin daukar dan wasan a kan kudi Fam miliyan 55 kamar yadda rohatanni suka nuna.
Sai dai dan wasan ya nuna bai da ra’ayin taka leda a kasar ta Ingila.
Wannan dai shi ne kusan karo na uku da Barcelona ke kasa kungiyar Chelsea a wajen sayen ’yan wasa, na baya-bayan nan dai shi ne dan wasan gaban Leeds United dan asalin kasar Brazil wato Raphinha da Barcelona din ta siya a lokacin da Chelsea ke dab da daukarsa.
Hakazalika shi ne dan wasa kusan na biyar da Xavi ya siyo a kakar wasar bana, a wani yunkuri na ganin ya dawo da martabar kungiyar ta Barcelona a idon duniya.