Getafe da Barcelona sun tashi 0-0 a wasan mako na 29 a gasar La Liga ranar Lahadi da suka kara a filin wasa na Coliseum Alfonso Perez.
Karo na hudu da kungiyar Camp Nou ta raba maki a gasar La Liga ta kakar nan, bayan fafatawa 29 da aka yi a gasar.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Karasa Zaben Gwamnan Adamawa A Abuja
- Dino Melaye ya zama dan takarar Gwaman Kogi a PDP
Barcelona ta ci karawa 23 a La Liga da canjaras hudu aka doke ta wasa biyu.
Kungiyar mai maki wadda Xavi ke jan ragama ta ci kwallo 53 aka zura mata tara.
Barcelona ta ci Getafe 1-0 ranar 22 ga watan Janairu a wasan farko a kakar bana a La Liga, inda Pedri ya ci mata kwallon saura minti 10 su je hutun rabin lokaci.
Ranar Asabar Real Madrid ta je ta doke Cadiz 2-0 a wasan mako na 29 da suka kece raini a La Liga tana ta biyu a teburi da maki 62.
Wadanda suka ci wa Real kwallayen sun hada da Nacho Fernandez da kuma Marco Asensio.
Getafe ta hada maki 31 kenan tana ta 16 a kasan teburin La Liga na kakar nan.
Barcelona za ta ziyarci Atletico Madrid a wasan mako na 30 ranar 23 ga watan Afirilu, yayin da Real Madrid da Celta Vigo za su kece raini a Santiago Bernabeu ranar 22 ga watan Afirilu.