Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta mika tayin yuro miliyan 40 don sayen dan wasan gaba na Bayern Munich Robert Lewandowski, da ke shirin raba gari da kungiyar mai doka gasar Bundesliga.
Barcelona na son kulla kwantiragin shekaru 3 ne da dan wasan kan yuro miliyan 35 sai kuma alawus na yuro miliyan 5, sai dai babu tabbacin zakarar ta Bundesliga ta amsa tayin kungiyar ta yankin Catalonia a Spain.
- Gidauniyar Zakkah da Wakafi ta koya wa ’yan mata 90 sana’oin hannu a Gombe
- DSS ta kama cibiyar rajistar zabe ta ’yan damfara a Nasarawa
Lewandowski dan Poland da ke shirin cika shekaru 34 a watan Agustan bana, na da sauran shekara guda a kwantiragin da ke tsakaninsa da Bayern duk da cewa ya fito karara ya bayyana ra’ayinsa na sauya sheka a wannan kaka.
A wata tattaunawarsa da manema labarai gabanin mika bukatar da Barcelona ta yi ranar Juma’a, ya ce yana fatan Bayern Munich ta amince da kudirinsa na sauya shekar.
A shekarar 2014 ne Lewandowski ya koma Bayern Munich daga Borussia Dortmund bayan karewar kwantiraginsa.
Barcelona dai na fatan Lewandowski ya doka mata wasannin rangadin shiga sabuwar kaka da za ta doka a Amurka ranar 26 ga watan Yuli.
Sai dai ko a lokacin da ya ke gabatar da Sadio Mane dan wasan da kungiyar ta sayo daga Liverpool kan yuro miliyan 35 a gaban manema labarai, shugaban Bayern Munich Oliver Kahn ya ce Lewandowski na da sauran shekara guda kuma basa tunanin rabuwa da shi kwana kusa.