Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sake tsawaita ratar da ke tsakaninta da babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid.
Wannan dai na zuwa ne bayan doke Villarreal da Barcelona ta yi a jiya Lahadi da ci daya mai ban haushi.
Kwallon da matashin dan wasa Pedri ya zura a minti na 18 da fara wasa ya bai wa Barcelonar damar ci gaba da jan zarenta na doka wasa na 6 a jere ba tare da an doke ta ba.
Barcelona wadda ta lashe gasar La Liga har sau 26, kwallaye 7 kadai aka iya zura mata cikin wannan kaka kuma shan kayenta na karshe shi ne a hannun Real Madrid cikin watan Disambar bara.
Yanzu haka dai Barcelonar na matsayin jagorar teburin na La Liga da maki 56 bayan doka wasanni 21.
Ita kuwa Madrid da ke biye da ita da maki 45 bayan doka wasanni 20, wato tazarar maki 11 daidai lokacin da aka kai tsakiyar wasannin wannan kaka.
Madrid wadda za ta dawo gida bayan nasarar lashe Gasar Kofin Duniya na Kungiyoyi da ta kara ita da Al-Hilal wanda aka tashi wasa 5 da 3, tana tunkarar babban kalubalen iya kamo abokiyar hamayyarta.
A ranar 15 ga watan nan ne tawagar ta Ancelotti za ta kara da Elche.