Kungiyar Barcelona da ke murza leda a Sfaniya ta nuna sha’awar daukar dan wasan Juventus na kasar Portugal, Cristiano Ronaldo.
Shugaban Barcelona, Juan Laporta na sha’awar kawo Ronaldo Camp Nou domin hada dan wasan da Lionel Messi su yi wasa a kungiyarsa a kakar wasa mai zuwa.
- Cutar amai da gudawa ta kashe mutum 119 a Kano
- An horar da kudan zuma don gano masu cutar Coronavirus
Laporta ya ce a shiye yake ya yi musayar ’yan wasan uku domin Juventus ta amince da bayar da dan wasanta na mai shekara 36.
Kafofin watsa labarai da daman a Turai sun ruwaito cewa, Laporta na shirin bayar da musayar Antoine Griezmann, Sergio Roberto da Phillipe Coutinho a cikin yarjejeniyar dauko tauraron dan wasan na kasar Portugal.
Sai dai akwa jan aiki babba a gaban Barcelona wajen dauko Ronaldo, duba da kyakkyawar dangartakar da ke tsakaninsa da abokiyar hamayyarta wato Real Madrid, inda ya shafe tsawon shekaru tara yana murza leda.
Idan kuma hakan ta tabbata ciniki ya fada, akwai babban kalubale a gaban Barcelona wajen iya daukar nauyin ci gaba da biyan albashi mai tsoka ga Messi da Ronaldo a lokaci guda, a yayin da manyan kungiyoyin kwallon kafa a duniya da dama ke fama da karancin kudi.