✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona: Kwalliya ta fara biyan kudin sabulu

Aubameyang ne ya zura wa Barcelona kwallo uku a raga.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta lallasa takwararta ta Valencia har gida da ci 4-1, wanda hakan ya bata damar komawa mataki na hudu a teburin gasar La Liga ta kasar Spain.

Wasan, wanda aka gwabza a yammacin ranar Lahadi a filin wasa na Mestalla da ke birnin Valencia na kasar, ya sa Barcelona ta gwada kwanjinta a kan Valencia.

Sabon dan wasan gaban Barcelona, Pierre-Emerick Aubameyang, ne ya zama zakara, inda ya zura kwallo uku a ragar Valencina.

Shi kuma dan wasan tsakiyar Barcelona, Frenkie De Jong, ya zura kwallo daya.

A yanzu dai Barcelona na da maki daya da Atletico Madrid, inda kowanensu ke da maki 42 a gasar.

Tun bayan yin cefane a watan Janairu da Barcelona ta yi, na sayo Aubameyang, Adama da Ferran Torres, kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.