Gwamnatin Jihar Nasarwa ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun gwamnati da na masu zaman kansu a dukkan fadin jihar saboda barazanar tsaro.
Gwamnatin ta ce daukar matakin ya zama wajibi a dukkana Kananan Hukumominta 13, da ma musamman babban birnin jihar wato Lafiya, saboda kare rayukan dalibai.
- Mafarauta sun tsinci katinan zabe sama da 300 a dajin Bayelsa
- An sayar da rigar da aka fara zuwa Duniyar Wata da ita a kan sama da N1bn
Daukar matakin ya biyo samun barazanar tsaro a cikin makon nan, musamman a yankin Babban Birnin Tarayya Abuja, inda ake garfabara lamarin zai iya shafar makwabtan jihohi.
Rufe makarantun dai na cikin irin sharwarwarin da aka yanke a taron Majalisar Zartarwar Jihar da ya gudana a Gidan Gwamnati ranar Laraba.
Da take yi wa ’yan jarida jawabi bayan kammala taron, Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Misis Fatu Jimaita Sabo, ta ce jihar ta dauki matakin ne cikin gaggawa saboda ya zamar mata tilas, musamman la’akari da kusancinta da Abuja.
Sai dai ta ce umarnin bai shafi daliban da suke azuzuwan karshe kuma suke zana jarabawa ba, musamman a makarantun sakandire.
Ta ce, “Muna kira ga iyaye da su kwantar da hankalinsu. Dukkanmu mun san Jihar Nasarawa kalau take, amma mun dauki wannan matakin ne don mu kiyaye rayuwar ’ya’yanmu.
“Muna kuma kira ga shugabannin makarantun da su tabbatar da cewa an rufe makarantun bisa ka’ida kuma cikin natsuwa.
“Har zuwa yanzu babu wata barazanar tsaro ta rai ko dukiya a jiharmu, kuma kamar yadda na bayyana a baya, wannan wani bangare ne na irin shirin ko-ta-kwanan da muke yi, musamman la’akari da yadda Gwamnatin Abdullahi Sule take ba sha’anin tsaro muhimmanci,” inji ta.