Ministan yada labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana barazanar ’yan ta’adda ta sace Shugaba Buhari da cewa abin dariya ne.
Ministan ya fadi hakan ne a Abuja a yayin da yake hira da ’yan jarida bayan fitowarsa daga taron Majalisar Zartaswa ta Kasa.
Lai Mohammed ya ce wadannan kalamai na ’yan ta’addan ba komai ba ne illa shirme da kuma farfaganda.”
Sannan ya ce, shugaban kasa na sane da abubuwan da ke faruwa kuma ana shirye-shiryen daukar matakan da suka dace domin ko a ranar Alhamis majalisar Tsaro ta Kasa za ta zauna kan al’amarin.
Minista ya kuma tabbatarwa da al’umar kasa cewa ba a zaune suke ba, “ Muna yin duk abin da ya kamata mu yi don ganin samar da tsaro a kasar nan.”
Ya kuma kwantar wa da al’umma hankali da cewa kowa zai gani a kasa, kan irin matakan tsaro da gwamnati za ta dauka wanda ba sai ya bayyana ba.