Barazanar harin ta’addanci ta tilasta masarautar Borgu da ke Karamar Hukumar Borgu ta Jihar Neja rufe manyan kasuwannin yankin.
Masauratar ta ce ta dauki wannan matakin ne domin kare rayukan jama’ar yankin daga ayyukan ‘yan ta’adda..
- Za mu kawo karshen matsalar tsaro a wata 6 in muka ci zabe – Kashim Shettima
- An ba hammata iska tsakanin Doguwa da Garo a Kano
Wannan na zuwa ne biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai sansanin sojojin da ke Wawa, daura da tafkin Kainji, a ranar Asabar.
Cikin wata sanarwar da ta fitar ta hannun Shugaban Kungiyar Matasan yankin, Muhammad Kabir, Masarautar ta ce ganin yadda zaman dar-dar ke dada kamari a tsakanin mazauna yankin ya sa aka dauki matakin rufe manyan kasuwannin yankin don kauce wa hare-haren ta’addanci.
Kazalika, masarautar ta kafa dokar hana fita daga karfe 9:00 na safe zuwa 6:00 na yamma don takaita zirga-zirgar jama’a a yankin.
Kazalika, ta ce daga yanzu tilas masu ababen hawa a yankin su tabbatar sun yi wa ababen hawan nasu lamba ko kuma a raba su da su.
Dokar takaita zirga-zirgar da kuma umarnin tabbatar da yi wa ababen hawan lamba sun soma aiki ne daga ranar Litinin, 31 ga watan Oktoba, in ji sanarwar.