✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

barayin shanu sun fallasa kansu a Neja

Shirin tantace Fulani makiyaya da Ardon garin Garatu ya bullo da shi ya tilasta wa wadansu barayin shanu biyar fallasa kansu tare da tuba daga…

Shirin tantace Fulani makiyaya da Ardon garin Garatu ya bullo da shi ya tilasta wa wadansu barayin shanu biyar fallasa kansu tare da tuba daga muguwar ta’asar da suka dade suna aikatawa a yankin.
daya daga cikin tubabbun barayin shanun mai shekara 31 wanda ya ki ya bayyana sunansa saboda kunya, ya shaida wa Aminiya cewa sun yanke shawarar tuba ce tun kafin shirin tantancewar ya gano su. “Mun san ba shakka idan ba mu tona wa kanmu asiri mun tuba ba, to babu shakka shirin tantacewar da Ardo ya bullo da shi zai gano mu. Shi ya sa muka yanke shawarar mu fito mu bayyana kanmu mu tuba kuma mu nemi jama’a su yafe mana,” inji shi.
Bafulatanin wanda ya ce ya yi hijira ne daga garin Kuta da ke karamar Hukumar Shiroro ya bayyana cewa a kwanan nan sun saci shanu uku a garin Garatu.
Ya nemi Ardon da Fulanin da suka yi wa satar shanun su yi musu afuwa, inda ya ba da tabbacin cewa za su ci gaba da bai wa Ardon goyon baya da hadin kai don fallasa sauran barayin shanu da suka ki mika wuya.
Da yake yi wa Aminiya karin bayani Ardon Garatu da ke karamar Hukumar Bosso a Jihar Neja, Alhaji Bello Ahmad ya ce sun bullo da shirin ne don tantance Fulanin da ke yankin da kuma sana’ar da suke gudanarwa. Ya ce suna daukar cikakkun bayanan Bafulatani da garin da ya fito da kuma dalilin da ya sanya ya yi hijira zuwa garin Garatu.
Ardon ya nuna farin cikinsa ganin yadda tun tafiya ba ta yi nisa ba, kwalliya ta fara biyan kudin sabulu, inda ya ce “Dalili kuwa shi ne a watan jiya na yi tunanin bullo da wannan tsarin kuma kafin in fara taron farko sai da na sanar da wadanda suka cancanta da suka hada da ’yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) da Hakimin Bosso, na yi musu bayani dalla-dalla sannan suka sa mini albarka kan lamarin,”inji shi.
Ya shawarci duk wani Bafulatanin da ke garin Garatu ya gaggauta zuwa fadarsa domin a tantance shi tare da yi masa rajistar kasancewarsa dan yankin Garatu. Kuma ya yi gargadin cewa duk wanda ya ki zuwa rajistar ya nuna cewa yana zaune ne a yankin da mummunar manufa.
Don haka ya tattara kayansa ya san inda dare ya yi masa don a cewarsa matakin da za su dauka a kansa ba zai yi masa dadi ba.