Ga alamu ana kara nuna damuwa ga karuwar ayyukan gungun masu dauke da makamai a yankin Arewa maso yamma da ayyukan masu satar shanu da masu garkuwa da mutane a jihohin kasar nan da dama.
Aminiya ta gano cewa harin baya-bayan nan ya nuna yadda yarjejniyar da aka cimma tsakanin gwamnati da masu gungun barayin ta ruguje.