Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama wasu mutum uku da ake zargin barayin mota ne aka kwato motocin sata a hannunsu a Zariya.
Kakakin rundunar, ASP Mansir Hassan ya ce an kama wadanda da ake zargin ne a yankin Agoro da ke Tudun Wadan Zariya.
- Hasashen muhimman abubuwan da za su faru a Kannywood a 2024
- Tsohon Shugaban ’Yan Sanda Alkali Ya Gina wa Al’umma Masallacin Juma’a
“A ranar 23 ga Nuwamba, 2023, ’yn sandan da ke hedikwatar shiyya ta Zariya, suka kama wani da ake zargin barawon mota ne a yankin Agoro, Tudun Wada, Zariya.
“Wanda ake zargin, mai shekara 28 dan Hayin Baki ne a yankin Birnin Gwari, kuma an kama shi ne da wata mota kirar Toyota Corolla da aka sace mai lamba Kano GWL 188 TT,” in ji shi.
Kazalika jami’an sashen Sabon Garin Zariya, sun kama wani mutum suka kwato wata motar sata kirar Toyota Corolla LE 2003 a hannunsa.
Wanda ake zargin ya ce ya sato motar ce a garin Kaduna, ya kawo ta Zariya da nufin sayar da ita.
’Yan sanda sun kuma kama wani barawon mota a Graceland da ke Zariya da wata mota kirar Toyota Hilux mai lamba Jigawa GML 40 AG.
“Wanda ake zargin ya ce ya sayi motar ne a hannun wani da bai bayyana sunansa ba.
“Za a gurfanar da su a gaban kotu domin girbar abin da suka aikata,” in ji sanarwar da kakakin ’yan sandan ya fitar.