Ta tabbata cewa wasu daga cikin jami’ai a gwamnatocin da suka gabata sun yi rud-da-ciki da dukiyar al’umma, inda a halin yanzu hukumar EFCC ke bincikensu. Abin tambaya a nan shi ne, irin wadannan barayi, ya dace su maido da dukiyar da suka sata kawai a kyale su ko kuwa a hada musu da hukunci, bayan an amshe dukiyar? Wakilanmu sun tattaro mana ra’ayoyin jama’a, kamar haka:
A karbe dukiyar kawai – Gambo Abdullahi
Hamza Aliyu, a Bauchi
Alhaji Gambo Abdullahi Bababa: “A gaskiya ina daya daga cikin wadanda suke goyon bayan a kama duk wanda ya saci kudaden talakawa a lokacin da yake rike da mukamin gwamnati, domin an dauki tsawon lokaci ana satar kudaden talakawa a Najeriya. Duk wanda aka ba shi wani mukami a gwamnati babu abin da yake buri kamar a kai shi inda zai yi sata amma abin da zan fada wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne, duk wanda aka samu ya saci kudin gwamnati a karbi abin da ya sata a sallame shi. Domin idan ya ce zai ci gaba da bincike tare da gurfanar da barayi a gaban kotu, to zai iya shafe sama da shekara shida bai kammala binciken ba; saboda an dauki tsawon lokaci ana cuwa-cuwa da kudaden al’umma.
’Yan kadan ne ba su da matsalar almundahana a Najeriya. Yaki da cin hanci da rashawa zai dauki tsawon lokaci, ko shekara takwas ya yi a kan mulki ba zai iya magance wannan matsala ba. Kuma duk wani talaka a Najeriya yana da tabbacin cewa Shugaban kasa ya zo da manufofi masu kyau na inganta rayuwar al’umma baki daya. Mafi yawan wadanda suka saci kudaden gwamnati ’yan Arewa ne kuma duk wata cuwa-cuwa da za a yi dole sai an hada da mutumin Arewa, domin shi ne ya san hanya.”
A karbi dukiyar a kyale su – danlami Adamu
Hamza Aliyu, a Bauchi
Alhaji danlami Adamu Muhammed: “Abin da zan fada game da wannan tambaya shi ne, gaskiya ina goyon bayan duk wanda hukuma ta samu da cin hanci da rashawa, a kwace dukkan kudaden da ya karba amma daga bisani a sallami mutum ba sai an gurfanar da shi a gaban kuliya ba. Idan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da kama wadanda suka yi wasoso da kudaden talakawa, gwamnatin za ta samu kudade masu dimbin yawa amma kuma za ta yi bakin jini a tsakanin al’umma saboda haka nake cewa idan an karbi kudaden babu laifi a sallami mutum ya koma cikin iyalansa. Yanzu haka ’yan Arewa ne gwamnati take ci gaba da kamawa amma muna fatar gwamnati za ta fadada shirin har zuwa Kudancin kasar nan. Satar kudin gwamnati cin amanar kasa ne. Mutum daya zai saci abin da sama mutum dubu talatin za su ci abinci, babu tausayi, babu imani. Satar kudaden gwamnati na daya daga cikin abubuwan da suka haddasa talauci da rugujewar tattalin arziki a Najeriya. Daga karshe ina ba da shawara ga wadanda suke rike da mukaman gwamnati, kowa ya shafa wa kansa ruwa domin yanzu Buhari ne yake mulki. Duk wanda aka samu da almundahana to tabbas zai dandana kudarsa.”
A karbi dukiyar kuma a hukunta mutum – Abdullahi Alkali
Nasiru Bello, a Sakkwato
Abdullahi Alkali: “Duk wanda ya mayar da dukiyar kasa wadda ya sata tare da yin almundahana, to bai kamata a kyale shi ba, yi masa hukunci ne zai gyara lamurran kasar nan. Don haka nake goyon bayan hukunta barayin kasa. Kan haka nake kira ga gwamnati ta yi tsayin daka wurin ganin an zakulo wadanda suka saci dukiyar kasa amma fa a yi adalci a cikin binciken, kada a dauki wasu a bar wasu. Don har yanzu ’yan jam’iyar PDP ne ake bincike, na APC sun tsallake ke nan? Don ko Jafaru Isa da aka gayyata don yana da alaka da Sambo ne. To haka bai dace ba, amma ina goyon bayan binciken tare da hukunta masu laifi da aka samu da satar. Bayan an karbe kudin, kada a bari su tafi abinsu, a hukunta su don na baya su kiyaye cewa akwai doka da hukunci gabansu. Cikin wannan muna bukatar a yi adalci.”
Wanda ya mayar a yi masa afuwa -Rukayya Hussaini
Nasiru Bello, a Sakkwato
Rukayya Hussaini: “Duk wanda ya mayar da dukiyar kasa, a bar shi ya tafi abinsa a ra’ayina saboda gaskiya akwai abubuwa uku da Shugaban kasa zai yi la’akari da su. Na daya lokaci, dole ne Shugaban kasa ya sani a yanzu ba shi da lokacin da zai hukunta wadanda suka saci dukiyar kasa, domin matsalolin da ya gada sun fi karfin ya mayar da hankali ga hukunta wadanda suka mayar da dukiya. In kuwa ya ce zai yi haka, gaskiya lokaci zai kure masa bai yi komai ba. Na biyu, shekarun wadanda suka yi barnar sun yi kadan, ma’ana duk mafi yawancinsu ba za su mayar da shekarun da suke da su ba a yanzu. Harkar iyali ta mamaye su ke nan. Don haka in ka ce ka kulle su, rayuwarsu da iyalan za ta kuntata kafin su bar duniya amma a karbi dukiyar su tafi, ya zama ciki lafiya baka lafiya. Na uku, yafiya ce kawai ke kawo arziki a kasa, ba a bari a kwashe gaba daya. Kan haka kawai a bar su su tafi bayan su mayar da dukiyar.”
A karbe kudin kuma a daure mutum – Bashir Lawal
Aliyu Babankarfi, a Zariya
Bashir Lawal Kwanyawa, Tudun Wada Zariya: “A hada duk tatike kuma a daure duk wanda ya debi kudin al’umma. A tatike shi, in ma abin da aka samu a hannun shi bai iya biya ba, a matsi ’yan uwansa ta yadda nan gaba in wani ya yi niyyar satar kudin gwamnati ’yan uwan nasa za su hana shi, koda magadansa kada a bar musu komai; ganin abin da ya faru da wani ko bayan haka a daure shi tsawon rayuwar sa, don ya zama darasi.”
A hada da hukunci bayan amshe kudin – Musa Dogara
Aliyu Babankarfi, a Zariya
Musa Dogara Zariya:
“A ra’ayina, duk wanda ya kwashi kudin al’umma ka ga ya dawo da dubu dari to ragowar biyu da hamsin na boye, don haka a ra’ayina a matse shi sai an tatse shi kaf sannan a daure shi; don ya zama darasi ga ’yan baya.”